Wani basarake ya nemi Kotun Shari’ar Musulunci da ke Sabon Gari a birnin Kano ta tilasta wa amaryarsa ta dawo gidansa a matsayin matarsa ko ta biya shi Naira miliyan 10 da ya kashe wajen aurenta.
Basaraken wanda shi ne Sarkin Gandun Zariya Alhaji Sama’ila Isa ya shaida wa kotun cewa bayan ya kashe kudi masu yawa a auren matar tasa mai suna Rahama Umar Bichi, kwanaki kadan sai ta gudu daga gidansa.
- Buhari ya dawo da Bashir Ahmad gwamnati, ya daga likafarsa
- Dan takarar Sanatan APC a Jigawa ya riga mu gidan gaskiya
Basaraken ya ce tun daga lokacin da amaryar tasa ta tare a gidansa sai ta shiga wasu halaye inda ake nemanta a rasa na tsawon kwanaki kafin daga baya ta dawo.
Kuma ya shaida wa kotun cewa kafin auren nasu ya kai matar tasa kasar Dubai da wasu kasashen ketare duk domin ya jawo hankalinta ga aurensa.
A zaman kotun lauyan mai kara Barista Naziru A. Uba ya nemi kotun ta tilasta wa amarya Rahama dawowa gidan mijinta ko ta dawo masa da Naira miliyan 10.
Ya ce sun shigar da kara a kotun Kano ce kasancewar wacce ake kara mazauniyar Jihar Kano ce.
Sai dai lauyan wacce ake kara Barista Ya’u Abdullahi ya shaida wa kotun cewa ba su san da wasu kudi da mai kara yake da’awar kashe wa wacce ake kara ba.
Ya ce kudin da suka sani shi ne kudin sadaki Naira dubu 100 wanda kuma a cewarsa a shirye suke su biya Naira dubu 10 a matsayin kudin Hul’i, amma batun kaya ta ci bilis lura da cewa kyauta ya yi mata a lokacin da yake neman auren.
Alkalin Kotun Mai shari’a Garba Hamza Malafa ya dage sauraren karar zuwa ranar 30 ga watan Agustan nan.