✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Basarake ya kamu da COVID-19 a Kaduna

Hakimin Kajuru a Jihar Kaduna, Titus Dauda ya harbu da cutar coronavirus. Basaraken ya shafe kusa mako guda yana fama da zazzabi kafin a kai…

Hakimin Kajuru a Jihar Kaduna, Titus Dauda ya harbu da cutar coronavirus.

Basaraken ya shafe kusa mako guda yana fama da zazzabi kafin a kai shi asibiti domin duba lafiyarsa.

A sanarwar da ya fitar da kansa ranar Asabar, hakimin ya ce gwajin da aka yi masa ya nuna ya kamu da cutar coronavirus.

“Sakamakon zazzabin da na yi fama da shi har na je asibiti aka yi mini gwajin COVID-19 ya fito kuma ya nuna inda dauke da cutar.

“Yanzu ina cibiyar killace masu cutar ta gwamnati ana duba ni. Ina rokon addu’o’inku gare ni da saruan masu cutar”, inji sanarwar.

Zuwa ranar Lahadi 16 ga Agusta mutum 1,766 ne suka kamu da cutar a Jihar Kaduna.