✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Barton da Benayoun sun yi cacar baki kan rikicin Isra’ila da Hamas

Joey Barton dan kasar Ingila da ke buga wasa a kolub din kueens Park Rangers ya yi yakin cacar baki da Yossi Benayoun dan Isra’ila…

Joey Barton dan kasar Ingila da ke buga wasa a kolub din kueens Park Rangers ya yi yakin cacar baki da Yossi Benayoun dan Isra’ila da ke buga wasa a kolub din Maccabi Haifa a Isra’ila kan rikicin da ya barke tsakanin Isra’ila da Hamas.
Tun da farko a shafinsa na twitter Barton ya rika neman Isra’ila ta daina kashe fararen hula da kuma kananan yara, al’amarin da ya sanya Benayoun ya mayar da martani da kakkausan lafazi.
Ya ce: “Harin da aka kai makarantar Beit Hanoun abin alla-wadai ne. Idan Isra’ila aka kai wa harin da yanzu Yammacin Turai sun shawo kan al’amarin. An kashe kananan yara. Dole a daina kai hare-haren.”
Hakan ya bata wa Benayoun rai, inda ya kira Barton da wawa.
“Lallai kai wawa ne, za ka ci gaba da kasancewa wawa har karshen rayuwarka. Wannan abin kaico ne.” inji Benayoun.
Barton ya ce ba yadda za a ce dole sai an tashi mutane daga muhallinsu saboda wani littafin tarihi da aka rubuta, don haka dole a kawo karshen zubar da jinin da ake yi.
Barton da Benayoun sun buga wasa a kulob din kPR tare, kuma abokan juna ne, amma rikicin Isra’ila da Hamas ya sanya su yakin cacar baki.