✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

barnar kindirmo

Wani Bafulatani ne ya ziyarci birni kuma da isarsa sai ya tarar da wani gida yana sheki, an yi masa farin fenti gwanin ban sha’awa. …

Wani Bafulatani ne ya ziyarci birni kuma da isarsa sai ya tarar da wani gida yana sheki, an yi masa farin fenti gwanin ban sha’awa.  Ya samu waje ya zauna, ya zuba wa gidan ido sai sharbar kuka yake. Mutane suka taru a kansa don jin dalilin da ya sa yake kuka. Da kyar aka shawo kansa ya fadi dalili kamar haka: “Wallahi wulakancin mutanen birni ne ya sa ni kuka, yanzu a ce a rasa inda za a yi barnar kindirmo sai a wannan gida. Dubi yadda aka bi shi da kindirmo aka shafe sai kyalli yake kamar ba su san darajar kindirmo ba!”
Daga Ahmed Garba Mohammed, 08028797883