✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Barka da warhaka Manyan Gobe 9

Barkanmu da warhaka Manyan Gobe, tare da fatan alheri kuma kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku wani labara na zaki da bera;…

Barkanmu da warhaka Manyan Gobe, tare da fatan alheri kuma kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku wani labara na zaki da bera; labarin na kunshe da darasin yadda alheri ba ya taba kadan. Asha karatu lafiya.
Taku Gwaggo Amina Abdullahi

Zaki da bera

A wani daji akwai wani zaki, wanda bai cika hulda da sauran namun daji ba. Wata rana sai barci ya dauke shi. Yana cikin barci mai nauyi, sai yaji wani abu ya fado akan hancinsa. Budar idonsa ke da wuya har ya kama abin da yake kan hancinsa. Ashe bera ne ya fada masa akan hancinsa.
Sai ya ce sai ya kashe beran ai wannan rashin kunya ce. bera sai ya fara karkarwa yana rokon zaki akan cewa ya yafe masa, wata ran shi ma zai taimaka masa.
Abin sai yaba zaki dariya. Akan ya za a yi bera karamar dabba ta taimake shi. Kawai dai sai ya bar bera.
Rannan wani maharbi ya sanya tarko domin neman naman daji. Sai zaki ya fada a cikin tarkon. Sai ya fara ihu. bera sai ya ji muryar kamar na zakin da ya kyale shi da ransa. Sai ya je inda ake ihun. Nan take sai ya gano cewa zakin ne ya fada tarkon maharbi. Sai ya je ya katse igiyar tarkon da hakoransa. Zaki sai ya yi farin ciki da hakan. Har ya gaya wa bara akan cewa bai taba zaton zai taba taimaka masa ba.
Da fatan Manyan Gobe zasu dau darasi akan wannan labarin.