✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Barka da warhaka Manyan Gobe 4

Assalamu alaikum Manyan Gobe, yaya hutu da sanyi? Da fatan ana nazarin karatu a lokacin hutu. A yau na kawo muku wani labarin ‘kasa da…

Assalamu alaikum Manyan Gobe, yaya hutu da sanyi? Da fatan ana nazarin karatu a lokacin hutu. A yau na kawo muku wani labarin ‘kasa da dutse’ labarin na kunshe da yadda rubutu a kasa bai cika mahimmamci ba da rubutun da aka zana a kan dutse. Asha karatu lafiya.
Taku: Gwaggo Amina Abdullahi

‘kasa da dutse’

Bala da Sule aminan juna ne sosai. Ran nan suka tafi daji domin neman itace sai musu ya kaure tsakaninsu. Nan take Bala ya  kwashe Sule da mari.
Abin sai ya bata wa Sule rai, amma sai yaki ya ramawa. Sai ya rubuta a kan kasa cewa “Yau aminina ya mare ni”. Hakan da ya yi yasa Bala yaji ba dadi.
Suna cikin tafiya sai suka ga rafi. Suka tsaya domin su yi wanka kafin su debo itace. Can sai Sule ya fara nutsewa a ruwa. Ganin hakan, Bala sai yaje da wuri ya taimakawa Sule. Sai ala ya sami kusa ya rubuta a kan dutse cewa “ Yau aminina ya ceci rayuwata”.
Ganin hakan, sai Bala ya ce “da na mare ka, ka rubuta a kan kasa cewa na mare ka. Yanzu kuma kayi rubutu akan dutse cewa na ceceka ko me yasa ka yi hakan?
Sai Sule ya ce idan an bata mana rai ya kamata mu zama masu hakuri. Shi yasa na yi rubutu akan kasa domin rubutu akan kasa ba shi da tasiri, kuma iska zai iya gogeta. Amma da ka taimaka min, nayi rubutu ne a kan dutse domin ba kyau mutum ya manta da alheri. Kuma ba a manta alheri komin kankantansa..
Da fatan Manyan Gobe za su koyi juriya da hakuri a duk lokacin da ransu ya baci. Kuma a san muhimmancin alheri.