✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Barka da warhaka Manyan Gobe 14

Ina muku lale-marhabin da sake saduwa da ku a wannan filin namu. Ina fata kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku labarin Salamatu…

Ina muku lale-marhabin da sake saduwa da ku a wannan filin namu. Ina fata kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku labarin Salamatu mai hakuri. Labarin na kunshe da yadda hakuri ke janyo ci gaba.
A sha karatu lafiya.
Taku: Amina Abdullahi

Labarin Salamatu mai hakuri

An yi wata mummunar ambaliya a wani kauye, a sakamokan hakan, sai yunwa ta shiga gari. An rasa abinci a kauyen; mutane sun wahala sosai. Ba a samun abinci a ko ina sai a gidan wani attajiri. Kullum sai a rika yin layi a gaban gidansa, domin karbar abinci. Mutane sukan yi fada da junansu domin su samu nasu rabon, sai Salamatu kullum ita ce a karshe, kuma sai a ba ta kadan.
Washegari kamar kullum, Salamatu ce ta karshe da aka ba biridi. Ta gutsiri biredin ke nan ta ci karo da sisi biyu a ciki. Sai ta koma ta mayar wa wannan attajirin. Abin sai ya ba shi mamaki kwarai da gaske. A irin yanayin da ake ciki, amma ta mayar masa da kudin. Daga nan sai ya ce ya bar mata wadannan sulallan, kuma ya kara mata wasu. Ya ce wa masu raba abinci su rika fara ba Salamatu abinci isasshe kafin a ba kowa a kauyen.
Da fatan Manyan Gobe za su dauki darasi daga wannan labarin. Masu magana sun ce mahakurci mawadaci.