✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Barka da warhaka Manyan Gobe 12

Assalamu alaikum Manyan Gobe, Fatan alheri gare ku, ina fata kuna cikin koshin lafiya. Labarinmu na yau a kan hakuri da hazaka da kuma cancanta…

Assalamu alaikum Manyan Gobe, Fatan alheri gare ku, ina fata kuna cikin koshin lafiya. Labarinmu na yau a kan hakuri da hazaka da kuma cancanta ne. Ya kunshi yadda dagewa da hakuri ke janyo wa mutum nasara a rayuwa. A sha karatu lafiya.
Taku;Gwaggo Amina Abdullahi.

Mai hakuri shi ke da nasara

An yi wani sarki mai wayo sosai a kasar sin. Rannan sai wazirinsa ya ce zai bar kujeransa saboda tsufa, kuma ba zai iya ci gaba ayyukan gidan sarautar ba. Sai sarki ya nemi wanda zai maye gurbin wazirin, don kuwa wazirin nasa mutum ne mai hakuri da hazaka a wajen aiki.
Bayan an kammala tantancewa ne sai aka ba sarki sunayen mutane biyu da Garba da Jauro. Kowa ya san Jauro mutum ne mai hazaka amma Garba na da kyuya. Sarki ya ce zai gwada su kafin ya nada daya daga cikinsu mukamin wazirin.
Sarki ya sanya su gasar tuka a kwale-kwale. Akan duk wanda ya riga tsallaka rafi shi za a nada sarautar Waziri.
Bayan sun shirya sai igiyar ruwa ta fara tumbatsa. Ganin haka sai Garba ya tsorata ya ce, ya hakura kuma ba zai halaka kansa a banza ba. Jauro ya dage har sai da ya tsallaka rafi kuma ya sake shiga ruwan ya ga cewa ashe kwakwa ce a rafin.
Sarki sai ya nada Jauro a matsayin wazirinsa.