✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Barka da Ranar ‘Yancin Kai!

A ranar Litinin da ta gabata ce Najeriya ta cika shekara 58 da samun ’yancin kai daga hannun Turawan Birtaniya, wanda ya faru a ranar 1…

A ranar Litinin da ta gabata ce Najeriya ta cika shekara 58 da samun ’yancin kai daga hannun Turawan Birtaniya, wanda ya faru a ranar 1 ga watan Oktoban 1960. Shekara 58 shekaru ne masu muhimmanci, musamman ga kasa da ke da akalla kabilu 250 da kuma addinai da al’adu mabambamta. Yadda Najeriya ta kasance kasa daya kadai abin a yaba ne idan aka yi la’akari da wasu kasashen da suka wargaje jim kadan bayan samun ’yancin kansu ko kuma wadanda ba su dade ba. Domin wannan dalili ne ya zama wajibi Najeriya ta yi murnar samun ’yancin kai a bana.

Idan muka dubi tarihi, babban makasudin gwagwarmaya da iyayen kasar nan na wancan lokacin suka sha wajen kwato ’yancin kan, shi ne domin a samu hadin kai. Wadanda suke kan gaba wajen kwato mana ’yanci sun hada da Sa Abubakar Tafawa Balewa da Sa Ahmadu Bello da Dokta Nnamdi Azikwe da Cif Herbert Macauley da Cif Anthony Enahoro. Sauran su ne Cif Obafemi Awolowo da Misis Funmilayo Ransome-Kuti. Duk da cewa wadannan mutanen suna da wasu harkoki na daban, babbar manufarsu ita ce hadin kan mutanen da suke zama tare a Najeriya ba tare da nuna bambancin kabila ko al’ada ko adddini ba.

A shekara 58 da suka gabata, kasar nan ta kasance a dinke domin har yanzu babu wani bangare da ya balle. Amma sai dai har yanzu ba a magance matsalar samar da cikakken hadin kai ba, duk da cewa an samar da dokoki da kudirori a kundin tsarin mulkin kasar nan wadanda za su taimaka domin cimma wannan buri. Matsalar rashin hadin kai ta shafi bangaren siyasa da tattalin arzikin kasa. Abin takaici ne yadda wadanda suke kan karagar mulki, wadanda su ne ya kamata su taimaka wajen samar da hadin kai, suke amfani da son kai wajen gudanar da ayyukansu.

A ’yan shakarun da suka gabata, kasar nan ta yi fama da matsalolin tsaro, inda wasu bangarorin kasar suke fama da ta’addanci da masu kokarin ballewa. A yankin Arewa maso Gabas, akwai Boko Haram; a Kudu maso Kudu akwai ’yan ta’addan Neja-Delta; a Kudu maso Yamma akwai Kungiyar Yarbawa Zalla ta OPC a da, sannan kuma a Kudu maso Gabas a da akwai MASSOB, wanda suka canja zuwa IPOB yanzu. Saboda irin wannan rikita-rikitar, sai rashin aminci ya tsanata a tsakanin ’yan Najeriya ta yadda ya kasance ana amfani da kabilanci wajen mu’amalar siyasa da tattalin arziki. Idan har kasar nan ta ci gaba a haka, lallai hadin kan kasar zai shiga cikin matsala, sannan za a tozartar da sadaukarwar da iyayen kasar suka yi a baya.

Da yake jawabi a kan wannan matsalar, a jawabinsa na 1 ga watan Oktoba na bara, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ce, “Ina jin takaicin yadda manyan mutanen wannan yankin ba sa jan hankalin matasansu masu zafin rai a kan abin da ya faru a Yakin Basasar kasar nan. Wadanda suke da rai lokacin yakin, ya kamata su fada wa wadannan matasa matsalar da aka shiga. A dukan mataki, tattaunawa tare da neman canji a kundin tsarin mulki ya kamata a rika yi ne ta hanyar sulhu a majalisa….”

Akwai alamomi da yawa da suka nuna cewa kasashe da yawa musamman a yankin Asiya wadanda suka samu ’yancin kai a lokaci daya da Najeriya sun shiga cikin kasashen da suka ci gaba. Suna shigo da kayayyakinsu Najeriya, duk kasar da ba ta da ingaccen bangaren masana’antu, to tana cikin matsala,  amma an bar Najeriya a baya wajen ci gaban tattalin arziki. Amma kuma har yanzu akwai sauran lokaci da za a iya yin gyara. Ga shi kuma bikin ’yancin kai na bana ya zo a daidai lokacin da ake shirye-shiryen zabe. A zaben 2019, ya kamata ’yan Najeriya su tabbatar da cewa sun zabi wadanda suke kaunar hadin kan kasar na da kuma tabbatar da ci gabanta ne. Duk wadanda suke da sha’awar tsayawa takara, ya kamata su zama a shirye wajen sadaurkar da kansu wajen habbaka tattalin arzikin Najeriya.

 

Barka da Bikin Samun ’Yancin Kai!