Rohotanni daga jihar Zamfara na bayyana cewa, yawan kashe-kashen da ‘yan fashi da makami suke yi a jihar, sanadiyyar fita da Gwamnan jihar ya yi ne na wasu kwanaki yasa lamarin ya karu.
Sama da mutum 40 aka kashe a cikin mako biyu a sababbin hareharen da ‘yan fashi da makami da barayin shanu suka kai wasu unguwanni da dama a jihar.
A ranar Litinin ne matasa a karamar hukumar Tsafe suka gudanar da zanga-zangar damuwa da yawan kashe-kashen da ake yi a Zamfara.