Garin Barikin Ladi, hedikwatar Karamar Hukumar Barikin Ladi, daya ne daya ne daga cikin garuruwan da suka yi fice wajen aikin hakar kuza a Jihar Filato da Najeriya baki daya, tun a zamanin turawan mulkin mallaka.
Shin yaya aka yi wa garin da suna Bariki, duk da cewa kalmar bariki a harshen Hausa tana da ma’anar duniyanci da wayewa da sauransu. Sannan wace ce Ladi, wadda ake danganta sunan garin da ita? Shin ita ce ta kafa garin.
Sannan lura da cewa Hausawa baki ne a Jihar Filato, shin Barikin Ladi garin Hausawa ne?
A kan haka ne Aminiya ta yi tattaki zuwa garin, ga kuma tsarabar da ta yi muku, kan asalin garin Barikin Ladi da yanayin rayuwar mutanensa da wasu abubuwa muhimmai masu kayatarwa game da shi.
Asalin kafuwar garin
Al’ummar garin sun shaida wa Aminiya cewa tun lokacin da turawa suka gano akwai kuza a wannan waje, daga nan ne suka fara kawo mutane suna aikin hakar kuza a wajen, shekaru 76 da suka gabata.
Game da sunan garin kuwa, Aminiya ta nemi jin yadda kalmar bariki ta shiga sunan garin.
Kalmar Bariki
Mai Unguwar Katakon Barikin Ladi, Ishak Ishak, ya ce “abin da ya sa ake amfani da kalmar bariki, shi ne wajen hakar Kuza, domin an dauka duk wajen hakar kuza bariki ce. Don haka aka sanyawa wajen Barikin Ladi.
“Ada idan ka bar karkara ka zo wani waje, sai a dauka ka je bariki ne.
Bayan Barikin Ladi, a yankin Barikin Ladi akwai Barikin Joji da Barikin akawu da wuraren hakar kuza da dama da ake kira Bariki, a wannan yanki.
“Idan masu hakar kuza za su zo nan, sukan ce bari su zo Barikin Ladi.
“Farkon sunan Barikin Lahadi ne daga baya sai aka cire ‘ha’ din aka bar shi Barikin Ladi.
Bariki Ladi, ana holewar kwarai da gaske domin ada mawakan Arewacin Najeriya babu ranar da ba za ka ga sun shigo wannan gari ba.
“To amma abin da ake nufi, mutumin da ya bar karkara ya zo yana hakar ma’adanai a wajen da yazo bariki ne. Don haka ake daukar duk wuraren hakar kuza a matsayin bariki.”
Wace ce Ladi?
Shin wace ce Ladi ko Lahadi? Majiyoyin a garin sun bayyana cewa akwai maganganu guda biyu game da kalmar Ladi a cikin sunan garin.
Kauli na farko shi ne, sunan garin ya samo asali ne daga wata mata da take sana’ar sayar da abinci ga leburori masu aikin hakar kuza, mai suna Ladi.
“A lokacin kasar Barikin Ladi tana karkashin Bauchi ne. Wata rana da Sarkin Bauchi ya zo rangadi wajen, sai ya samu mutane sun tafi wajen aikin hakar kuza, sai wannan mata kadai ya samu.
“Ya tambayi sunanta, sai ta fada masa cewa sunanta Ladi. Ya tambaye ta ina mutane suke, ta ce sun tafi aiki. Shi ne sai ya sanya wa wannan gari sunan Barikin Ladi,” in ji majiyar.
Amma a kauli na biyu, wanda ake ganin ya fi karfi, shi ne, ya samo asali ne daga ranar Lahadi kuma leburori ne suka sanya wa garin wannan suna.
“A tsarin turawa a lokacin barikokin Kuza, guda 6 suke da su. kuma kowace bariki, akwai ranar da ake biyan leburorin da suke yin aikin hakar Kuza.
“A lokacin suna biyan leburorin da suke aikin hakar kuza, a wannan waje a ranar Lahadi. Saboda ana biya a ranar Lahad, shi ne leburorin suka sanya wa wannan gari sunan Barikin Ladi. Kuma ana ce wa wannan magana tafi karfi, kan asalin sunan garin na Barikin Ladi.”
Shi ma da yake zantawa da Aminiya, kan wannan al’amari, Mai Unguwar Katakon Barikin Ladi, Ishak Ishak, ya bayyana cewa lokacin da turawa suka zo wannan yanki, akwai wani dattijo mai suna Baba Sale.
“Wannan dattijo, shi ne yake tafinta tsakanin Turawa da leburori masu aikin hakar Kuza, kuma turawan suka ce, ya samo masu wani mutum da zai rika kawo masu dabbobi da kayan abinci da za su rika saye.
“Shi ne ya samo wani mutum mai suna Alhaji Muhammed Dikkwa, domin ya yi masu wannan aiki, kuma daga baya suka nada shi, Sarkin wannan gari na farko.
“A lokacin da ya tsufa, sai aka ba shi shawarar ya sauka ya barwa dansa, mai suna Alhaji Adam Muhammed sarautar wannan gari. Wannan da nasa shi ne har yanzu yake sarautar wannan gari. A halin yanzu ya shekara 53, yana sarautar wannan gari.”
Kabilun Barikin Ladi
Mazauna sun bayyana Aminiya bayanin cewa a da a garin Barikin Ladi akwai yawanin kabilun Nijeriya, kama daga Fulani da Hausawa da Terawa da Barebari da Yarbawa da Ibo da sauran kabilun Arewaci da kudanci.
“A da a wannan gari babu kabilar Najeriya da babu. Kuma har yanzu, akwai wadannan kabilu a cikin wannan gari. Amma yanzu ba su da yawa kamar da,” in ji shi.
Yanayin rayuwa
“Har yanzu yanayin rayuwa a wannan gari akwai dadi,” a wannan gari in ji Mai Unguwa Ishak Ishak.
Wani dattijo, Malam Yahuza Abubakar, ya shaida wa Aminiya cewa babban abin sha’awa ada a Barikin Ladi, shi ne zamantakewa a tsakanin al’ummar gari.
Malam Yahuza ya ce, “A da kowa yana shiga gidan kowa, a ci abincin juna. Amma yanzu abin ya baci.
“Kuma mafi yawan dattawa, duk da ba a zaune wuri daya, amma har yanzu, akwai kyakyawar dangantaka. Matasa ne kawai, suka fi daukar abin da zafi.”
Abin ban sha’awa
Game da yanayin hadin kai da ayyukan al’umma, basaraken ya ce, “abubuwan da aka rasa yanzu a wannan gari shi ne, a da akwai yarda da aminci da juna, amma yanzu babu wannan. Yanzu an sami rauni tsakanin Musulmi da sauran ’yan kasa, a wannan yanki.”
Sannan ana samun kayayyaki da araha a wannan gari, musamman kayan lambu irin su tumatur da kabeji da wake.
Basaraken ya ce yanzu wani lokaci, idan aka zo yin aikin da ya shafi al’umma baki daya, sai a yi watsi da al’ummar garin Barikin Ladi.
Sana’o’i
Mai Unguwa Ishak Ishak ya shaida mana cewa sana’o’in al’ummar garin sun hada da na gargajiya da na zamani.
A cewarsa, “Ana harkokin noma da kiwo. Ada ana noman damina ne kawai, a wannan gari amma yanzu ana noman lambu mai yawa. Yanzu Hausawa da Fulani da ’yan kasa kowa ya rungumi noman lambu a wannan gari.
“Akwai mutanen jihohin Jigawa da Kano da suke zuwa sana’ar lambu a wannan gari.
“Akwai masu sana’o’in gargajiya da dama da har yanzu suke ci gaba da yi a wannan gari kamar wanzamai da makera da mahauta da kuma ma’aikatan gwamnati da ma’aikatan kuza. Haka kuma akwai ’yan kasuwa.