✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Barcelona za ta iya lashe La Ligar bana —Ronaldinho

A halin yanzu Barcelona mai maki 60 ita ce ka zaman ta biyu a gasar La Liga.

Tsohon tauraron Barcelona Ronaldinho ya bayyana kwarin gwiwar cewa kungiyar za ta iya nuna wa Real Madrid zarra wajen lashe kofin gasar La Liga ta bana.

Ronaldinho ya bayyana haka ne, bayan wasan da Barcelona ta doke Lavente da kwallaye 3-2, yayin karawa mai zafi da suka yi a daren ranar Lahadi.

Aubameyang, Pedri da kuma Luke de Jong ne suka ci wa Barca kwallayenta uku, yayin da Morales da Roger suka ci wa Lavente nata.

A farkon kakar wasa ta bana dai, sai da Barcelona ta koma matsayin ta 9 a gasar La Liga a yayin da take karkashin tsohon kocinta Ronald Koeman wanda aka sallama a cikin Oktoban shekarar bara, tare da maye gurbinsa da Xavi, wanda da zuwansa ya maido da karsashin tsohuwar kungiyar ta sa.

A halin yanzu Barcelona mai maki 60 ita ce ke zaman ta biyu a gasar La Liga, yayin da Real Madrid ke kan gaba da maki 72, tazarar maki 12 tsakaninsu.