✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Barcelona ta lashe gasar Laliga na bana

  Kungiyar Barcelona ta lashe gasar Laliga na bana bayan ta lallasa kungiyar Deportivo La Coruna da ci 4 da 2, inda Messi ya zura…

 

Kungiyar Barcelona ta lashe gasar Laliga na bana bayan ta lallasa kungiyar Deportivo La Coruna da ci 4 da 2, inda Messi ya zura kwallaye har uku a ragar Deportivo a wasan.

Wannan ne karo na 25 da Barcelona ta lashe wannan gasar, takwas kasa da kungiyar Real Madrid da ta lashe gasar sau 33.

A yanzu haka dai Barcelona na tafarkin kafa wani babban tarihi, domin har yanzu ba a doke ta ko wasa daya ba a kakan bana na wannan gasar, kuma saura wasa hudu kacal a kammala.

Sai dai suna da wasa da Real Madrid a ranar Lahadi mai zuwa.