✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Barcelona ta fara yunkurin sabunta wa Messi kwantaragi

Duk da yake kwantaragin Lionel Messi a kulob  din FC Barcelona sai a shekarar 2018 zai kare, Shugaban kulob din Maria Bartomeu ya ce tuni…

Duk da yake kwantaragin Lionel Messi a kulob  din FC Barcelona sai a shekarar 2018 zai kare, Shugaban kulob din Maria Bartomeu ya ce tuni kulob din ya fara yunkurin sabunta kwantaragin dan kwallon.  Ya ce nan ba da dadewa ba ne za su sanar da tsawon shekarun da suka kara wa Messi don ganin ya cigaba da yi wa kulob din kwallo har illa masha Allah.
Messi, dan shekara 29, kwantaraginsa za ta kare ne a shekarar 2018.
“Messi dai kwantaraginsa za ta kare ne a shekarar 2018 amma muna yunkurin sabunta masa kwantaragi don ya ji dadin cigaba da yi mana kwallo”, inji shugaban a hirar da ya yi da wata jarida a Sifen.
Kawo yanzu Lionel Messi yana haskakawa a gasar rukuni-rukuni na Sifen da aka fi sani da La-Liga tun bayan da aka fara gasar kimanin makwanni biyu da suka wuce bayan ya taimaka wa FC Barcelona lashe wasanni biyu da ta yi.
Lionel Messi dai ya koma Ajantina don taimaka wa kasarsa hayewa gasar cin kofin duniya, inda ake sa ran Ajantina za ta kece raini da Uruguay da kuma benezuela.