Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta kammala daukar kyaftin kuma dan wasan gaban Arsenal, Pierre-Emerick Aubameyang, bayan warware kwantaraginsa da kungiyar.
Dan wasan mai shekara 32 ya rattaba hannun zama a Barcelona har zuwa karshen kakar wasanni ta 2025.
- Daliba Mafi Hazaka ta Duniya ta lashe wani sabon kambu
- Kisan Hanifa: An mayar da shari’ar gaban Babbar Kotu
Aubameyang ya sauka a birnin Barcelona na kasa Spain a ranar Litinin, inda aka masa gwajin lafiya kafin daga bisani ya sanya wa kungiyar hannu.
Aubameyang ya samu matsala da Arsenal wanda hakan ya kai ga karbe kambun kyaftin daga hannunsa, sannan kungiyar ta daina sanya shi a wasa sakamakon laifi da ya yi mata.
Daga karshe ya cim-ma yarjejeniya tsakaninsa da Arsenal, inda ya warware kwantaraginsa wanda hakan ya ba shi damar zuwa Barcelona a kyauta.
Kafin karewar watan Janairu, an yi hadar-hadar ’yan wasa a nahiyar Turai, inda ’yan wasa suka rika sauya sheka daga wata zuwa wata kungiyar.