✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Barbara Bush, matar tsohon shugaban kasar Amurka ta rasu

Barbara, matar George Bush Babba, kuma uwar Bush karami, ita kadai ce matar da aka rantsar da mijinta da danta a idonta a matsayin shugabannin…

Barbara, matar George Bush Babba, kuma uwar Bush karami, ita kadai ce matar da aka rantsar da mijinta da danta a idonta a matsayin shugabannin kasa a Amurka.

Misis Bush ta sha fama da rashin lafiya na dan wani lokaci, kafin rasuwarta a cikin wannan makon.

A zamaninta a fadar White House a farkon shekarar 1990 zuwa 2000, ayyukanta sun wuce na matar dan siyasa da aka sani a bisa al’ada.

Haka kuma ta sha nuna adawarta kan nuna bambanci da adawarta kan wasu manufofin mijinta a jami’iyyar Republican.

Tarihinta 

Ita dai Barbara Bush wacce ake kira Piece an haifeta ne a ranar 17 ga watan Yuni na shekarar 1925 kuma ta rasu ne a ranar 17 ga watan Afrilun bana, wanda hakan ya nuna cewa ta rayu na tsawon shekara 93 ke nan a duniya.

An haife ta ne a birnin New York, kuma ta kammala karatunta ne makarantar Ashley Hall da ke Kudancin Carplina. Sun hadu da Maigidanta George Herbert Walker Bush ne tana ‘yar shekara 16 a duniya, sannan suka yi aure a garin Rye da ke birnin New York a shekarar 1945. Suna da ‘ya’ya shida tare, ciki har da tsohon Shugaban kasar Amurka George W Bush da tsohon Gwamnan Jihar Florida wanda ya yi gwamna na 43, Jeb Bush.

A lokacin da Barbara ke Uwargidan Shugaban kasa, ta assasa Gidauniyar Barbara Bush Foundation For Family Literacy domin taimakon ilimin duniya baki daya.

Tun a shekarar 2008 ta fara fama da matsananciyar jinya, inda har aka mata tiyatar hanji, sannan kuma ta sha fama da ciwon tari na Nimoniya. Hakanan kuma ta sha fama da ciwon zuciya, sannan da ciwukan suka yi yawa kuma suka kamari, a watan Afrilun bana iyalan gidan Bush suka fitar da sanarwar cewa Barbara ta gaji da zuwa asibiti, don haka za ta ci gaba da zama a gida tana jinya kawai ba za ta sake zuwa asibiti ba. Sannan daga bisani ta rasu a gida a ranar 17 ga watan Afrilu, kuma za a bikin binne ta a ranar 21 da watan na Afrilu a cocin St. Martin’s Episcopam da ke Houston.

Daga cikin wadanda suka aike da sakon ta’aziyarsu akwai Shugaban Amurka na yanzu Donald Trump da Uwargidansa Melania Trump. Da tsofaffin shugabannin Amurka irin su Jimmy Carter da Bill Clinton da Barack Obama da dai sauransu.