✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Barazanar tsaro ta tilasta sauya wurin bikin yaye sabbin lauyoyi a Abuja.

An bukaci ’yan uwan sabbin lauyoyin su kaurace wa harabar taron da a dauke daga harabar makarantar

Makarantar Koyon Aikin Lauya da ke Abuja ta sauya wurin gudanar da bikin yaye sabbin lauyoyin daga harabar hedikwatar makarantar da ke Bwari.

Babban Daraktan makarantar, Farfesa Hayatu Isa Ciroma ya bayyana sakatariyar makarantar da ke bayan hedikwatar Hukumar EFCC a Abujan a matsayin sabo wurin taron.

“An dauke gudanar da bikin yaye sabbin lauyoyi na bana daga makarantar da ke Bwari zuwa Sakatariyar da ke bayan Hukumar EFCC ranar 27 ga watan Yuli,” a cewarsa.

Jagororin shirya bikin dai sun shawarci ’yan uwan wadanda za a yaye da su nisanci wurin, domin iya sabbin lauyoyin da aka amince wa ne kadai za su shiga harabar.

Duk da hukumomi ba su bayyana dalilan samun sauyin ba, amma hakan ba ya rasa nasaba da matsalar tsaro da Birnin ke fama da shi a yanzu.

Wata majiya ta bayyanawa wakilinmu cewa ’yan ta’adda sun aikawa hukumomar gudanarwar makarantar takardar barazanar hari, wanda ya sanya suka sanar da rundunar sojin Abujan.

Rahoton da makarantar ta kai ne ya sanya aka tashi wani Kyaftin da wasu sojoji biyu domin gudanar da bincike, amma a hanyarsu ta komawa ’yan bindiga suka kashe su.

Sufeto-Janar na ’Yan Sandan Najeriya, Usman Alkali Baba, ya bayyana cewa tuni an jibge jami’an tsaro a birnin don haka al’umma su kwantar da hankalinsu.