Darakta-Janar na Hukumar Kula da Albarkatun ruwa ta Najeriya (NHSA), Moses Beckley, ya yi hasashen tumbatsar Kogunan Neja-Binuwai da sauran idanun ruwan kananan koguna a daminar bana, inda ya yi nuni da cewa ambaliya na iya far wa jihohin da ke kusa da wadannan kogunan. Ya yi wannan hasashen ne a lokacin kaddamar da Kundin nazarin ambaliya na shekara-shekara (AFO) a Abuja ranar 25 ga Yulin 2016.
Jihohin da ke tattare da hadarin ambaliyar a cewar Hukumar NHSA, sun hada da Neja da Binuwai da Sakkwato da Anambara da Imo da Kogi da Kuros Riba da Yobe da Ogun da Kebbi da Osun. Sauran su ne Zamfara da Katsina da Kwara da Adamawa da Bauchi da Barno da Gombe da Taraba da Filato da Nasarawa. Sannan kuma da Ribas da Edo da Bayelsa da Dalta da Legas da Ondo da Akwa-Ibom da Ebonyi da Abiya da Jigawa da Kano. Hukumar ta kara da Legas da Fatakwal da Kalaba da Bayelsa da Dalta da Ondo, wadanda aka yi nunin cewa ambaliyar za ta tunkare su ne ta gabar kogi, saboda tumbatsar teku da murdin igiyar ruwa. Tuni dai jihohin da suka hada da Kano da Kuros Roba da Jigawa suka yi fama da ambaliya a wannan shekarar.
A nata bangaren kuwa, Hukumar kula da yanayi ta kasa (NIMET )ta fitar da sanarwa a makon da ya wuce cewa, za a samu ambaliya da zaizayar kasa a wasu sassan kasar nan, musamman yankunan da ke kusa da gabar kogi a karshen wannan shekarar. Darakta-Janar na Hukumar ta NIMET, Dokta Anthony Anuforom, wanda ya bayyana al’amari, ya ce: “al’amarin ambaliya da zaizayar kasa a gaba da yankunan gabar kogi ba za a iya kauce wa aukuwarsa ba, don haka ake da matukar bukatar fadakarwa, ta yadda za a rage illoli tare da hadarin da ke tattare da asarar rayuka da dukiya, musamman a yankunan da suke tattare da hadarin ambaliya a gabar kogi da ke tumbatsa.
Fadakarwa da ankararwa game da karatowar ambaliya na tunatarwa ne kan irin mummunar illa da ambaliyar ta yi a shekarar 2012, wadda ta shammaci kasar nan. Mafi yawan al’ummomin da ke garuruwa da yankunan karkara da biranen tumbatsar ruwan sama ta mamaye su. kwararrun masana sun yi ikrarin cewa, ambaliyar shekarar 2012 ita ce mafi muni da ta taba aukuwa cikin shekara 40 da ta gabata, inda ta cutar da mutane kimanin miliyan bakwai da ke daukacin jihohi 30 daga cikin 36 na Najeriya. kiyasin kimar darajar kudin asarar da aka yi an kimanta shi da Naira tiriliyan biyu da biliyan 600.
Ga dukkan alamu, jihohi da dama sun kwance lif tun bayan matsalar ambaliyar 2012, domin jihohi kadan ne daga cikin 36 suka dauki kwararan matakan shawo kan ambaliya. Wasu daga cikin matakan da za su taimaka sun hada da: gina wurin tara ruwa don shawo kan ambaliyar ruwan (irin wannan ruwan za a iya tace shi don amfanin al’umma); katangar kariya a gabar kogi: a fadada magudanan ruwa; a samar da bular buttutu a kan tituna; dasa itatuwa a mafi yawan wuraren da ke tattare da hadarin ambaliya; a gina kananan matattarar ruwa da madatsu, wadanda za a iya amfani da su wajen noma da kamun kifi. Babu wata hujja da ta nuna cewa an yi amfani da irin wadannan matakan kariya a Najeriya a matsayin daukin gaggawa tun bayan shekarar 2012.
Muna kira ga gwamnatocin jihohi da su hanzarta wajen gina matattarar ruwa a wasu zababbun wurare, inda za a iya tura ruwa don yin wasu ayyuka da suka hada da noman rani da kiwon kifi da sauransu. Sannan a sake tsugunnar da ’yan Najeriya da ke zaune a yankunan da ke tattare da hadarin ambaliya. Hakki ne da ya rataya akan gwamnati ta kare wadanda take mulka daga musifu.
Rashin tausaya wa al’umma ne idan har jihohin da Hukumar kula da yanayi ta NIMET ta ce ambaliya za ta shafe su, su jira musifar ta auku kafin ta sake tsugunnar da mutane. Kuma akwai fargabar ruwa zai iya share gonaki, al’amarin da ka iya haifar da karancin abinci. Muna shawartar gwamnati ta tara abinci, ta alkinta shi a wani wuri kebabbe, ta yadda za a shawo kan matsalar karanci abinci.
Sannan muna kira kan adauki mataki na tsawon lokaci wajen shawo kan ambaliya. A aiwatar da dokar hana yin ginin gidaje a hanyoyin ruwa da ke daukacin fadin kasar nan. Gwamnati ta hana cunkoson gidajen marasa galihu a birane, ta hanyar tabbatar da cewa an tsara biranwe yadda ya kamata, an samar da hanyoyi da magudanai don hana yin gine-gine harbutsai na marasa galihu.
Barazanar karatowar ambaliya
Darakta-Janar na Hukumar Kula da Albarkatun ruwa ta Najeriya (NHSA), Moses Beckley, ya yi hasashen tumbatsar Kogunan Neja-Binuwai da sauran idanun ruwan kananan koguna a…