✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Barayin waya 3 sun shiga hannu a Bauchi

Rundunar ta ce za ta gurfanar da su a kotu da zarar ta kammala bincike.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Bauchi, ta cafke wasu barayi biyu kan satar wayar hannu guda tara a jihar.

Rundunar ta kuma kama wani mutum daya da ake zargi da satar babur a jihar.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Ahmed Wakil, ya fitar a ranar Lahadi a Bauchi.

Ya ce jami’an rundunar sun kama wadanda ake zargin ne a bayan filin wasa na Abubakar Tafawa Balewa dauke da wayoyin da sata.

“Wadanda ake zargin sun bai wa wani ma’aikacin gwamnati cin hancin kudi don hana kama su,” in ji shi.

Rundunar ’yan sandan, ta ce ta kuma kwato buhun tabar wiwi da kuma kudi N78,000 da suka bayar a matsayin cin hanci domin a sasanta lamarin.

Wakil ya ce jami’an rundunar sun kuma kama wani da ake zargi a laifin daba wa wani ɗan acaba wuka a hanyar Ningj zuwa Bauchi.

“Wanda ake zargin ya aikata wannan danyen aikin ne don kwace babur din dan acaban,” in ji shi.

Kakakin ya ce kwamishinan ’yan sandan jihar, Auwal Musa, ya bayar da umarnin gudanar da bincike kan lamarin, inda ya ce nan ba da jimawa ba za su gurfanar da wadanda ake zargin a kotu.