✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Barayin shanu sun shiga hannu a Kaduna

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kaduna, Ahmad Abdurrahman ya ce rundunar  ta yi nasarar kama wadansu barayin shanu biyu a dajin Buruku da ke Karamar Hukumar…

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kaduna, Ahmad Abdurrahman ya ce rundunar  ta yi nasarar kama wadansu barayin shanu biyu a dajin Buruku da ke Karamar Hukumar Chikun a jihar.

Ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya sanya wa hannu wanda aka raba wa manema labarai. A cewarsa, ’yan sanda tare da hadin gwiwar ’yan sintiri a yankin ne suka yi nasarar kama wadanda ake zargin.

Ya ce jami’an tsaro sun kuma yi nasarar kwato shanu 55 da barayin suka gudu suka bari, bayan an yi ba-ta-kashi a tsakaninsu da ’yan sandan.

“Yanzu haka 12 daga cikin shanun an samu masu su. Buhari Mohammed daga Buruku ya gane shanunsa shida, shi kuma Mustapha Lawal daga Mando ya gane shanu biyu sai Hassan Umar daga Maidaro ya gane hudu.

“Sauran shanu 43 da tumaki 9 suna hannun ’yan sanda, muna jiran masu su domin su kawo shaidun da za su nuna dabbobinsu ne mu mika musu abinsu,” inji shi.

Kwamishinan ya bukaci kafafen watsa labarai su taimaka wajen yada labarin domin a gano masu dabbobin.