Rundunar ’yan sandan Jihar Osun ta tabbatar da cewa masu garkuwa da aka kubutar daga hannun wasu mutane a Osogbo, sun samu tabin hankali bayan dukan kawo wuka da aka musu.
Wadanda ake zargin sun sha dukan tsiya ne a hannun mazauna yankin Gbodofon, bayan sun yi yunkurin yin garkuwa da wani karamin yaro.
- An kone wanda ake zargi da satar babura kurmus a Osun
- An ba wadanda suka saci kayan tallafin Osun sa’o’i 72 su dawo da su
- An cafke dan sanda da satar waya da kudi a Osun
Ba tare da bata lokaci ba mutane suka taru suka fara lakada musu duka ba kakkautawa.
Mutanen yankin sun yi yunkuri kona su, amma shugabannin yankin suka huna, suka damka wadanda ake zargin ga ’yan sanda.
’Yan sanda daga Babban Ofishin ’yan sanda da ke Oja Oba sun isa wurin a kan lokacin kafin mutanen su kone su.
Shugabannin yankin sun yaba wa ’yan sandan da suka karaso wajen a kan lokaci tare da hana mutane daukar doka a hannunsu duk da irin yadda aka yi kokarin hana su.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Yemisi Opalola, ya ce bayan gudanar da bincike an gano wanda ake zargin sun samu tabin hankali sakamakon dukan tsiya da suka sha a hannun mazauna yankin.