Wasu mutum hudu da ake zargi da kona shagunan teloli 10 bayan sun yi sata a tsohuwar Kasuwar Gombe sun shiga hannun ’yan sanda.
Kwamishinan ’yan sandan jihar, Oqua Etim ne ya gabatar da wadanda ake zargin ga manema labarai inda ya ce a ranar 3 ga watan Agusta 2023 ne wasu mutum 18 daga tsohuwar kasuwar suka kai rahoto ofishin shiya na Gombe cewa wasu bata-gari sun fasa musu shaguna 15 suka musu sata sannan suka cinna wa 10 daga cikin shagunan wuta.
- Tsadar rayuwa: Mun kosa jihohi su raba mana tallafin Tinubu —Talakawa
- Gidan yari zan jefa duk wanda ya karkatar da kayan tallafi —Bago
A cewarsa bayan samun rahoton ne jami’an sa suka tsunduma bincike inda suka kama wasu mutum 4 da ake zargin suna da hannu a wannan aika-aikar.
Wadanda ake zargin ’yan shekara 16 zuwa 19 ne kuma a yayin bincike an gano kekunan dinki guda biyu kirar Butterfly da zannuwa guda 7 da ba’a dinka ba a hannunsu.
Ya ce da zarar rundunar ta kammala bincike za ta tura wadanda ake zargin zuwa Kotu.
Daga nan sai ya hori al’umma da su dinga sa ido suna lura da duk wani wanda ba su yarda da shi ba wajen, domin kai wa jami’an tsaro rahoto.