✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Barawon garin kwaki a Kalaba ya sha da kyar

Wani matashi a kasuwar Marian Kalaba, Jihar Kurosriba, mai suna John Ator ya tsallake rijiya da baya, inda har an rataya masa taya a wuya…

Wani matashi a kasuwar Marian Kalaba, Jihar Kurosriba, mai suna John Ator ya tsallake rijiya da baya, inda har an rataya masa taya a wuya za a kona shi sakamakon zarginsa da satar buhun garin kwaki a kasuwar, amma sai wadansu ‘yan kasuwa suka kwace shi suka mika shi ga ‘yan sanda.

Matashin ya auna arziki ne bayan da wasu fusatattun matasa suka kwace barawon daga hannun ’yan sintiri na kasuwar, bayan da suka kama shi bisa zargin sace buhunan kwaki biyu.

Wani dan kasuwa da ya zanta da wakilinmu ya ce sun dade a wannan kasuwa ana yi musu satar buhunan kwaki bayan sun rufe shagunansu sun koma gida, duk da kasancewa akwai masu gadi da kuma ’yan sintiri amma duk da haka al’amarin bai canja ba. Dalili ke nan ya sanya suka shirya yin kwantan bauna, suka yi sa’ar kama Ator. Majiyar labarin ta ci gaba da cewa, barayi sun addabi sashen kasuwar sayar da kwaki, da aka ga abu ya ki karewa sai aka shirya mutane suka labe a wurare daba-daban na sashen kasuwar garin rogo, aka yi katarin kama wannan barawo da dubunsa ta cika.

Aminiya ta tambayi wanda ake zargi da satar buhunan garin rogon, John Ator ko me ya sa shi satar kwaki? Sai ya ce: “Ba ni da kudin mota da zan tafi kauyenmu bikin zuwan sabuwar doya da kowane matashi dan kauyenmu ke halarta kuma abin gori ne a ce duk wani dan kauyenmu wannan lokaci ya yi bai je gida ba wajen shagalin. Ni kuma da na ga ba hanyar da zan samu kudi cikin sauki, ya sa na yanke shawarar yin sata.”