An cafke wata mata mai shekaru 23 bayan ta sace sace jaririya mai kwana uku a Jihar Oyo.
Rundunar ’yan Sandan Jihar Oyo ta ce matar da dubunta ya ciki, ta sace jaririyar ce mako guda bayan ta yi bari.
- DAGA LARABA: Daga Lahadin Nan INEC Za Ta Rufe Rajistar Katin Zabe
- Majalisar Wakilai ta yi watsi da kudirin kafa dokar haramta Acaba
Kakakin rundunar, SP Adewale Osifeso, ya ce an kamo ta ne a unguwar Badore da ke karamar hukumar Ajah a Jihar Legas da jririyar a hannunta, a ranar 19 ga watan Yuli.
Ya ce a yayin bincike sun gano cewa mahaifiyar jaririyar ta aininhi Monsurat Lateef da ke unguwar Ogbere a karamar hukumar Ona Ara ta jihar, ta haife ta ne a ranar 16 ga watan Yuli a wani asibiti da ke Ogberen.
Yadda aka sace jaririyar
A a ranar 19 ga wata da aka sace jaririyar kuma ta kai ta allurar riga-kafi ne inda suka hadu da wacce ake zargin.
“Ta je mata ne a matsayin mara lafiyar da ta je neman magani a Babban Asibitin Abaemu da ke Ona Ara, sai dai gaskiyar abin da ya kai ta shi ne hoto da gwaje-gwaje sakamakon barin da ta yi”, in ji kakakin.
“A hirarsu ne ta bayyana wa Monsurat cewa tana son dawowa garin Ibadan daga Legas inda ta ke zama, kuma tausayi ya sanya Monsurat cewa za ta taya ta nemo gida, har da ba ta masauki a gidanta, sakamakon nemo gidan da ya kai su dare.
“Washegari da misalin karfe 1:00 na rana ne amincewa ta sanya mahaifiyar jaririyar barin wacce ake zargin ta tafi da ita a bayanta domin yin sayaya, ita kuma daga nan ta tsere da ita”.
Kakakin dai ya ce za su maka matar a kotu da zarar sun kammala bincike.