Sanata mai wakiltar Kano ta Arewa a Majalisar Dattijai, Barau Jibrin, ya fasa yin takarar Gwamnan Kano inda yanzu ya sayi fom din komawa kujerar shi ta Sanata.
Hakan dai na nufin a yanzu Barau, wanda shi ne Shugaban Kwamitin Kasafin Kudi na majalisar zai fafata ne da Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje a neman kujerar.
- Hutun Sallah ne ya jawo wahalar man fetur — NNPC
- NAJERIYA A YAU: Yadda Sauyin Yanayi Zai Shafi Daminar Bana
A karshen mako ne dai wani taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a Jihar ya amince Gandujen ya nemi kujerar Sanatan, yayin da suka kuma amince da Mataimakin Gandujen, Nasiru Yusuf Gawuna a matsayin dan takarar Gwamna.
Sanata Barau dai na daya daga cikin jagororin kungiyar ’yan majalisa ta G-7 daga Jihar, wacce ta fafata rikicin shugabanci da tsagin Gwamnan.
Ya dai yanke shawarar fasa neman kujerar Gwamnan ne kwana daya bayan amincewa da Gawuna ya tsaya takarar.
A yayin zantawarsa da wakilinmu ta wayar salula, Sanatan ya tabbatar da sayen fom din don sake neman kujerar.