Wani rahoton Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), ya bayyana cewar shan barasa na kashe mutum miliyan 2.6 a duk shekara.
WHO, ta ƙara da cewa yayin da adadin waɗanda suka mutu ya ragu kaɗan a ’yan shekarun nan, amma ta ce ba za a lamunci ci gaban ƙaruwar ba.
- Jami’in Kwastam ya mutu yayin zaman kwamitin majalisa
- Tsige Sarkin Musulmi: Ka rika bincike kafin yin magana —Gwamnan Sakkwato ga Shettima
Rahoton hukumar na baya-bayan kan barasa da lafiya, ya ce barasa na janyo mutuwar kusan mutum ɗaya cikin 20 a duniya a kowace shekara, ta hanyar tuƙi cikin maye, tashe-tashen hankula da kuma cututtukan da barasa ke haifarwa.
Kazalika, rahoton ya danganta mutuwar mutum miliyan 2.6 da shan barasa a 2019 – sabuwar ƙididdigar da aka samu, wadda ta kai kashi 4.7 cikin 100 na mace-macen duniya a wannan shekarar.
A cewar rahoton, kusan kashi uku cikin huɗu na waɗanda suka mutu, maza ne.
“Amfani da barasa yana cutar da lafiyar mutum sosai, yana ƙara hatsarin kamuwa da cututtuka da kuma haifar da mutuwar miliyoyin da za a iya rigakafi kowace shekara,” in ji Darakta Janar na WHO, Tedros Adhanom Ghebreyesus.
Ya yi nuni da cewa an sa6mi raguwar yawan shan barasa da cutarwa a duniya tun daga 2010.
“Amma batun lafiya da zamantakewar jama’a saboda amfani da barasa ya kasance abu mai girman da ba za a yarda da shi ba,” in ji shi.
WHO, ta ce mafi yawan adadin mace-macen sakamakon shan barasa a 2019 – kashi 13 cikin 100 – na cikin mutane masu shekara 20 zuwa 39.
Ana danganta sha da kashe yanayin lafiya, gami da cutar hanta da wasu cututtukan daji.
A mace-macen da barasa ta yi sanadi a 2019, rahoton ya nuna cewa kimanin mutum miliyan 1.6 sun faru ne sakamakon cututtuka marasa yaɗuwa.
Daga cikin waɗannan, 474,000 sun fito ne daga cututtukan zuciya da jijiyoyin jini, 401,000 daga cutar daji da kuma 724,000 daga raunuka, gami da hatsarin ababen hawa da kuma cututtuka.
Har wa yau, rahoton ya ce shaye-shaye na sa mutane su iya kamuwa da cututtuka kamar su tarin fuka, HIV da kuma ciwon hunhu.