Ga duk mai bibiyar yanayin siyasar Kano ya san cewar tun tale-tale cike take da abubuwa na ban sha’awa da mamaki da takaici da hargagi da kuma ban haushi. Tarihi ya nuna salo da gogewar kanawa wajen siyasa tun zamanin siyasar jamhuriyya ta daya, har zuwa yau, a baya na taba rubuta wata makala makamanciyar wannan a harshen Ingilishi mai taken ‘The political bolatility of Kanawa’ wacce aka buga a tsohuwar jaridar Daily Triumph, inda na ambato irin tirka-tirka da rashin tabbas da ke cikin siyasar Kano, wacce jama’a ke cewa sai Kanon.
A halin yanzu haka an samu wani sabon lamari da ya dauki hankalin jama’ar ciki da wajen Jihar Kano, inda aka samu baraka ta fili tsakanin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da ubangidansa, kuma tsohon Gwamnan Jihar Kano, jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso. Tabbas abin da mamaki da kuma takaici, kodayake dama akwai yiwuwar faruwar hakan, in an yi duba da irin yadda masu fashin baki a harkar siyasa ke ambata rashin tabbas a tafiya ta gamayya a siyasance, inda suke cewa, babu aboki na din-din-din kuma babu abokin hamayya na din-din-din a siyasa (no permanent friend and no permanent enemy in politics), lamarin da ya jawo cece-ku ce a tsakanin al’umma, musamman ganin yadda suka zamto abokan tafiyar siyasa na tsawon lokaci kuma ba a taba jin kansu ba, tun dawowar siyasa a shekarar 1999, sai a makon da ya gabata ta tabbata akwai sabani mai karfi a tsakaninsu, wanda a da ake yi wa kallon ingiza mai kantu ruwa; magoya bayansu ke yi ta hanyar rura wutar rikicin a kafafen watsa labarai na zamani, kwatsam sai ga shi kowannensu ya amayar da abin dake cikinsa don tura wa dan uwansa sakon kar ta kwana.
Wannan lamarin ya faru ne a lokacin da shi tsohon gwamnan, kuma Sanata a yanzu ya kai ziyarar gaisuwar ta’aziyya bisa rashin mahaifiyar Gandujen, inda jama’a ke ganin shi kwankwason ya aike da wani sako, wanda ke nuni da cewar har yanzu fa shi ne uba, kuma jagora a jam’iyyar APC a Kano, bisa la’akari da irin gangamin da ya yi na magoya baya zuwa garin Ganduje, al’amarin da jagorancin jam’iyyar da kuma wasu al’umma ke alamta shi da tsagwaron rashin da’a, har ma jagororin jam’iyyar suka kira taron gaggawa na manema labarai, inda suka bayyana matsayinsu a kan hukunta Kwankwaso a kan abin da ya aikata, musamman yadda ta’aziyya ta kai shi wajen. Koma dai meye rigima tsakanin yaro da ubangida ba yau farau ba a Kano da ma kasa baki daya.
A jamhuriya ta biyu hakan faru tsakanin Mallam Aminu Kano da Dokta Abubakar Rimi, wanda ya yi sanadiyyar faduwar Rimi a zaben 1983. A lokacin siyasar 1991 rigimar ta faru tsakanin jagororin jam’iyyar SDP mai yawan magoya baya a Kano da kuma dan takararta na gwamna, wanda shi ma ya yi sanadiyyar faduwarta wanwar a zaben gwamna. A sake kwata irin wannan tsakanin Mallam Musa Gadabe, Dokta Abubakar Rimi da shi Kwankwason, wanda ya yi sanadiyyar barin Rimi da Musa Gwadabe daga jam’’iyyar PDP zuwa ACD a shekarar2007.
Haka zalika ba kadai a siyasar Kano hakan ke faruwa ba, kowa yasan irin tirka-tirkar siyasar da ta faru tsakanin Yariman Bakura da Shinkafi a Jihar Zamfara kamar yadda ya faru tsakanin Mala Kachalla da Ali Modu Sheriff a Jihar Borno da sauransu. Sai dai lamarin Kwankwaso da Ganduje ya fi daukar hankalin jama’a ganin tsawon shekaru 16 ba a taba jin kansu ba. Batu na gaskiya ba za ka iya dora wa kowannensu laifin dungurungum ba, sai dai a iya cewa, matsalar jagorancin jam’iyya a matakin jiha shi ya assasa wannan rigimar da ta jawo maida martani a tsakaninsu, kodayake tun a bara ake ta rade-radin cewar dole tasa Kwankwaso ya bai wa Ganduje takara ba don son ransa ba, ana kuma cewa, shi ma Gandujen dole tasa yake bin Kwankwasiyya ba don son ransa ba. Duk wannan zargin na iya zama gaskiya; idan kuwa hakan ne, to tabbas batun samun sabani na san za a rina. Abin da ya sa na ce haka kuwa, bai wuce ganin yadda Kwankwaso ya tsaya tsayin daka, ya kuma jajirce wajen assasa akidar siyasarsa ta Kwankwasiyya, har ta samu karbuwa ba a jihar Kano kadai ba. Dalilin da zai jajirce don tabbatar da ita ta hanyar ganin kansa a matsayin uba, kuma jagora a jam’iyyar APC a Jihar Kano, wanda kuma hakan zai wahalar yiwuwa bisaa tsarin uwar jam’iyyar da ta bai wa gwamnonin jihohi damar jagorantar jam’iyyar a jihohinsu, tsarin da ya bai wa shi kansa Kwankwason damar zama jigo, kuma uba a jam’iyyar ta APC duk da cewar ya shigo ya tarar da iyayen da suka yanke wa jam’iyyar cibiya ba ma a Jihar Kano ba, har a kasa baki daya, amma hakan tasa dole suka fita suka bar masa jan ragama a matsayinsa na gwamna.
Wadannan al’amura da suka faru a baya sun zamo madubin dubawa ga duk wanda zai yi fashin baki game da wannan barakar da ta kunno kai tsakanin Kwankwaso da Ganduje, musamman don tabbatar da ka’ida da bin dokokin jam’iyya. Ni dai a ganina wannnan neman girman na jiga-jigan yan jam’iyyar ba shi ne abin da ya kamace su ba, madadin su maida hankali wajen kawo wa jiharsu da jama’arsu cigaba mai dorewa, musamman a wannan lokacin da rayuwar jama’a ke cike da kalubale da kunchi ta fuskar tattalin arziki. Lokaci ya yi kusa, musamman ganin ko shekara daya ba a yi da kafa sabuwar gwamnatin ba. Ya kamata su nuna wa jama’arsu halin dattako, sanin makamar aiki da kuma aiki da tarbiyya don ciyar da Jihar Kano gaba.
Ina bai wa ’yan siyasa shawara da su rika aikata uzurorinsu na siyasa a lokacin da ya dace, a kuma muhallin da ya kamata, su kuma kasance masu kai zuciya nesa. Su kuwa talakawa, su zamo masu fatan alheri ga shugabanninsu, musamman ganin irin wannan rigimar kan fada kan talakawa ne, don masu iya magana na cewa, idan manyan giwaye na fada ciyawa ce ke shan wahala, saboda haka ina kira ga Kwankwaso da Ganduje su yi karatun ta nutsu, su maida hankali kan samarwa jama’arsu jindadi da walwala maimakon rikicin cikin gida da ba zai haifar da da mai ido ba.
Mudassir ya rubuto daga NTA Zaria. [email protected]
barakar Kwankwaso da Ganduje, a rina
Ga duk mai bibiyar yanayin siyasar Kano ya san cewar tun tale-tale cike take da abubuwa na ban sha’awa da mamaki da takaici da hargagi…