Hukumar Kula da Ayyukan ’Yan sanda a Najeriya (PSC), ta sanar da dakatar da batun daukar sabbin kuratan ma’aikata da ta sanar a makon jiya.
Sanarwar na zuwa ne kasa da sa’o’i 24 da Babban Sufeto Janar na ‘yan sandan Najeriya, Usman Alkali Baba, ya fusata kan tallar da hukumar ta fitar na neman duk masu bukata su nemi gurbin aikin ta hanyar mika mata bayanansu a shafinta na yanar gizo.
- An tsaurara tsaro a Kano bayan rahoton kai hari hedikwatar ‘yan sanda
- ’Yan sandan da ke karbar na-goro sun ba ni kunya —Alkali Baba
Sai dai Alkali Baba ta bakin Kakakin rundunar, Olumuyiwa Adejobi, ya bukaci ’yan Najeriya da su yi watsi da tallar da aka sanya a wasu jaridun kasar ciki har da Jaridar Daily Trust.
Shugaban ‘yan sandan ya ce, tallar ba ta da alaka da rundunar ’yan sandan Najeriya, kuma hakan sam bai dace da tsarin daukar aikin ‘yan sanda ba.
Da yake mayar da martani a ranar Talata, Kakakin Hukumar PSC, Ikechukwu Ani, ya tabbatar da cewa akwai an samu sabani tsakanin Hukumar da rundunar ‘yan sanda, inda ya ce za a warware komai nan ba da dadewa ba
Sai dai ya bukaci ’yan Najeriya da suka nuna sha’awar shiga aikin ’yan sandan da su tsahirta da neman aikin yanzu.
Ani ya bukaci masu sha’awar aiki da su fara bai wa hukumar damar sasanta sabanin da ke tsakaninta da rundunar ‘yan sandan.