Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya rantsar da sabbin kwamishinoni kasa bakwai a Hukumar Tsara Alashi ta Kasa (RMAFC), kwana biyar kafin ya sauka daga mulki
Buhari ya ba su rantsuwar aiki ne gabanin fara taron Majalisar Zartarwa ta Kasa ta karshe a gwamnatinsa a ranar Laraba, a Fadar Shugaban Kasa.
Sabbin Kwamishinonin da aka rantsar su ne: Hawa Aliyu daga Jihar Jigawa da Rekiya Haruna (Kebbi) da Ismaila Agaka (Kwara) da Sanata Ayogu Eze (Enugu) da kuma Peter Opara (Imo).
Sauran su ne Kolawole Abimbola daga Jihar Oyo, sai kuma Ayuba Ngako daga Yankin Babban Birnin Tarayya.
- Rancen Paris Club: Gwamnati za ta dawo wa jihohi kudadensu
- WhatsApp ya bullo da tsarin gyara saƙon da aka aika — Zuckerberg
A yayin zaman, Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo ya mika rahoton kwamitin da ya jagoranta kan inganta bangaren lafiya, domin samar da jadawali da nagartaccen tsarin kula da lafiya ga daukacin ’yan kasa cikin sauki.