Bankunan kasuwanci a a Najeriya sun ci gaba da ba wa kwastomomi tsoffin takardun N1,000 da kuma N500 da aka sauya wa fasali.
Aminiya ta gano akalla bankuna uku a Abuja da wani guda daya a Kano sun koma ba wa kwastomominsu tsoffin takardun kudin da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya sauya wa fasali a ranar Litinin.
- Atiku ya jagoranci zanga-zangar neman INEC ta soke zaben shugaban kasa
- Kotu ta aike da matasan da suka kone ofishin INEC kurkuku
A yayin da bankunan kasuwanci ke ba da tsoffin kudin a Kano, a Abuja, bankuna irin su GT sun bi sahu, ko da yake wasu irin su Polaris ba su fara biyan tsoffin kudaden ba.
Wani jami’in banki da ya nemi a boye sunansa ya ce tsoffin N200 suke biya, “saboda har yanzu ba mu samu wani umarni game da abin za mu yi ba.”
“Matsalar ita ce kafin mu karbi tsoffin kudin daga kwastomomi sai an cike takardar da CBN ta tanadar saboda hakan,” a cewar wata majiya a bankin.
Kawo yanzu dai babu tabbaci daga CBN cewa ta umarci bankunan su ci gaba da ba wa jama’a tsoffin kudin ba.