✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bankin Barclays zai daina kasuwanci a Afirka

A ranar Talatar da ta gabata ne Bankin Barclays na kasar Birtaniya ya ce zai daina gunadar da harkokin kasuwancinsa a nahiyar Afirka bayan da…

A ranar Talatar da ta gabata ne Bankin Barclays na kasar Birtaniya ya ce zai daina gunadar da harkokin kasuwancinsa a nahiyar Afirka bayan da ya shafe fiye da shekara 100 yana kasuwanci a nahiyar.
Barclays ya bayar da wannan sanarwar ce a wani bangare na sauye-sauyen da yake yi bayan da hannayen jarinsa suka ragu da kusan rabi a cikin shekara guda.
Bankin ya ce zai rage kashi 62 cikin 100 na jarinsa da ke Afirka a cikin shekara biyu zuwa uku masu zuwa domin ya kara mayar da hankali a kan ayyukan da suka fi zama wajibi.
Shugaban Barclays, Maria Ramos, ya ce bankin ya dauki matsayin ne ba wai domin hasashen da ake yi kan makomar tattalin arzikin Afirka ba ne.
Masu mu’amala da bankin a nahiyar sun haura miliyan 12.
Kuma wasu masana suna ganin daukar wannnan mataki ba ya rasa nasaba da yadda kudin kasashen nahiyar yake ci gaba da faduwa, musamman ma kasar Afirka ta Kudu.