Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar ya ce ba a ga watan Shawwal ba a Najeriya ranar Asabar, saboda haka azumi 30 za a yi a Najeriya.
Sarkin, wanda kuma shi ne Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci a Najeriya (NSCIA), ya ce hakan na nufin sai ranar Litinin, biyu ga watan Afrilun 2022.
Hakan dai ya biyo bayan rashin samun rahoton ganin watan Shawwal na shekarar 1443 a ranar Asabar, 29 ga watan Ramadan, daidai da 30 ga Afirilun 2022.
Sanarwar wacce Shugaban kwamitin kuma Wazirin Sakkwato, Farfesa Sambo Wali Junaid ya sanya wa hannu ta nuna cewa za a cika Azumi zuwa 30 a ranar Lahadi.
Ya ce Sarkin Musulmi ya amince da rahoton da kwamitin ya bayar, don haka Sallah sai ranar Litinin, biyu ga watan Mayun 2022.
Sarkin Musulmin ya roki gafarar Allah a watan Ramadan da fatan samun zaman lafiya a Najeriya.