✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bana goro ya yi tsadar da bai taba yi ba – Bilya dan Oron

Tun yaushe ka fara sana’ar goro? Yau dai na kai kimanin shekara 12. Na ji masu cin goro idan sun zo saye suna cewa daushen…

Tun yaushe ka fara sana’ar goro?

Yau dai na kai kimanin shekara 12.

Na ji masu cin goro idan sun zo saye suna cewa daushen goro, ko za ka yi mana karin bayani dangane da nau’ukan goro?

Sunayen goro kala-kala ne, bangare-bangare ne haka. Akwai Fari akwai kuma Ja, akwai Maku. Shi Maku an fi samunsa a nan bangaren Kalaba amma sauran sassan irin su Ondo da Osun, ana samun Fari zalla ana kuma samun  Ja zalla; haka kuma ana samun Ja da Fari a hade.

Kamar a nan Kalaba fa, wane iri aka fi samu?

A nan Kalaba kuma an fi samun Ja da Maku.

Na ji mutane suna cewa daushen goro, shin me ya bambanta shi da sauran goro kuma me ya sa ake kiransa daushe?

Bambancin da ya sa ake kiransa daushe shi ne, yana dan daukar lokaci ne na ajiya, domin wani ana ajiye shi shekara daya, wani wata 8, wani wata 9 kafin ya zama ainihin daushen.

Yaya kakar goro ta bana ta shigo maku?

Kakar goro dai bana za a iya cewa ta zo da tangarda saboda ainihin yadda ya saba fitowa da yawa, bana bai fito hakan ba.

Me kake jin ya hana shi fita da yawa?

Wannan kuma daga Allah ne, ba mu sani ba. Duk dai hasashe an yi an gama, lokacin fitar ya yi bai fito da yawa ba. Ana ta hasashen lokaci kaza zai fito, har yanzu bai fito yadda ake so ba, har yanzu a haka ake.

Yaya za ka kwatanta mana kasuwar ta bana da kuma lokacin da ka fara wannan harka tsawon shekarun da ka ambata?

To, ni dai tsawon shekarun da na fara, gaskiya bana ya zo da yanayi wanda ba a gane masa; har ma wadanda suka rigaye mu sana’ar sun ce mana tsawon shekarun da suka kwashe suna sana’ar ba a taba samun goro ya yi tsada kamar bana ba. Ya yi daraja fiye da sauran shekaru da suka gabata.

Da ka ce ya zo da wani irin yanayi da bai taba zuwa da shi ba, kamar me kake nufi ke nan?

Yanayi ne na tsada da ya zo da shi da bai taba zuwa da shi ba kuma mutane ba su tunanin zai yi irin wannan tsadar.

Ko tsada ta hana maku saye ku aika shi zuwa kasuwannin da kuke aikawa?

A’a, ba ta hana ba sai dai ta hana yawan goron a kasuwa. Ka ga maimakon da za ka iya sanya dan kankanen jari a kasuwa, yanzu sai ka sa kudi masu yawa kuma bai saya maka kayan da yawa ba.

Na ga ana lodin goro a manyan motoci, wace kasuwa ake kai wa, ta gida ce ko ta waje?

Mu dai iyakacinmu da shi mu kai Kano, to amma akan zo Kano daga wurare da dama a saya.

korafin tsadar goro da ake yi, yaya ka tunkari kasuwar ta bana?

Yadda na tunkari kasuwar goro a bana sai da na dan tsaya na duba yanayin kasuwar, inda muke saye muke sayarwa saboda ina tunanin kada in zo ban san ainihin abin da ake sayarwa ba in saya; gudun kada in yi kasuwa da kai sai da  na ga kamun ludayin kasuwar, yadda zan sayar sannan kuma na zo nan na duba kamun ludayin wannan kasuwar tukunna na saya na aika.

Daga lokacin da ka fara wannan harka ko kana fuskantar wani abu?

Eh! Alhamdu lillahi, ina fuskanta ba laifi. Daidai gwargwado ana samu.

Ke nan  kwalliya tana biyan kudin sabulu?

Eh ! Alhamdu lillahi.

Wane kalubale ka taba fuskanta a wannan harka?

Ta konewar goro, gaskiya sau daya na taba fuskantar wannan matsala ta konewar goro daga nan kuma Allah Yana kiyaye ni. Ka san idan goro ya kone asara ce mai goro ya tafka ta kudi da kadara.