✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ban yi nadamar tattaki don Buhari ba – Sulaiman Hashim

Matashin nan da ya yi wa Shugaba Buhari tattaki daga Legas zuwa Babban Birnin Tarayya, Abuja ya musanta jita-jitar da ake yadawa a kafafan sadarwa…

Matashin nan da ya yi wa Shugaba Buhari tattaki daga Legas zuwa Babban Birnin Tarayya, Abuja ya musanta jita-jitar da ake yadawa a kafafan sadarwa cewa wai ya ce ya yi nadamar tattakin da ya yi wa Shugaba Buhari.

Ya ce jita-jitar ba ta da tushe, domin har gobe yana da soyayyar da yake yi ga Shugaba Buhari saboda salon mulkinsa na taimakon ƙasa ne kuma talakawan Najeriya suna tare da shi. “Nan ba da jimawa ba zan jagoranci wani gangami na talakawa domin nuna wa jama’ar ƙasar nan soyayyar talakawa na nan daram-dam tare da Shugaba Buhari. Kuma masu rubuta wasiƙa irin su Obasanjo da ma muna sane da su kuma da yawansu za su ƙara bayyana. Su ne irin mutanen nan da kyakyawan tsarin gwamnati ya hana su tsula tsiyarsu. Abin da ya kamata jama’a su gane, ko a baya ma ba su suka zaɓi Shugaba Buhari ba, nufi ne na Allah kuma zaɓin talaka,” inji shi.

Ya ce gangamin da talakawa suka yi wa Shugaba Buhari a Jihar Nasarawa ’yar manuniya ce kuma Gwamnan Jihar, Tanko Al-Makura, dole a yaba masa saboda irin hoɓbasar da ya yi. “Sai dai mu a Arewa muna fuskantar ƙalubale da dama domin gwamnonin Kudu sun fi na Arewa yi wa talakawansu abin a zo a gani. Amma mu a Arewa, matasa sai dai a ba su makamai su zamo ’yan bangar siyaysa ba tare da kawo tsarin da za su amfana ba. Don haka dole ne matasanmu su san ciwon kansu su watsar da bangar siyasa, su nemi na kansu su kuma sani ƙuri’arsu ita ce ’yancinsu ba banga ko gabar siyasa ba,” inji shi.

Sulaiman Hashim ya ƙara da cewa manyan alƙawuran da Shugaba Buhari ya yi guda 4 ne, waɗanda suka haɗa da yaƙi da cin hanci da rashawa da samar da tsaro da bunƙasa noma da tattalin arzikin ƙasa kuma ya yi abin a zo a gani a dukansu, idan aka yi la’akari da irin yanayin ƙasar nan a lokacin da ya karɓi ragamarta.