Tsohon Shugaban Nijeriya, Goodluck Jonathan ya ce dala biliyan 49.8 ba ta ɓace ba a zamanin mulkinsa kamar yadda tsohon gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN) Sanusi Lamiɗo Sanusi ya yi iƙirari a 2014.
Aminiya ta ruwaito Jonathan yana faɗin hakan ranar Alhamis a Abuja a yayin bikin ƙaddamar da wani littafi da tsohon Gwamnan na CBN ya wallafa.
- An kashe ƙasurguman ’yan bindiga Sani Black da Kachalla Makore a Zamfara
- EFCC ta bankaɗo sabuwar badaƙalar fiye da N100bn kan Yahaya Bello
Tsohon shugaban ƙasar ya ce ba zai yiwu maƙudan kuɗaɗe irin wannan sun ɓace a wata ƙasa, amma kuma ta iya ci gaba da biyan albashi ba.
“Ina ganin akwai buƙatar in amsa wasu maganganu da ya faɗa a cikin littafin, musamman waɗanda suke da alaƙa da ni.
“Ya ce an cire shi ne saboda fitar da maganar da ya yi a kan ɓacewar kuɗi dala biliyan 49.8 daga lalitar gwamnati.
“Gaskiya wannan ba haka ba ne. Ba cire shi aka yi ba, dakatar da shi aka yi,” in ji shi.
“Kafin mu gama bincike kan iƙirarin da ya yi kuma wa’adinsa ya ƙare, wataƙila da mun dawo da shi. Amma har yanzu ban yarda cewa dala biliyan 49.8 ta ɓace ba.
“Da farko an ce dala biliyan 49.8 ce ta ɓace, sai kuma aka ce dala biliyan 20, daga baya kuma aka koma ana cewa dala biliyan 12. Saboda ban ma san wane iƙirarin ne na daidai ba.
Jonathan ya ƙara da cewa bayan binciken ƙwaƙwaf da aka yi, “da rahoton ya fito, dala biliyan 1.48 ne rahoton ya ce ba a tabbatar ba, amma nan ma sai aka buƙaci kamfanin NNPC ya biya kuɗin a asusun Gwamnatin Tarayya.”