An yi zargin Ambasada Kabiru Rabi’u Dansitta, wanda kwanan nan aka sallame shi daga cibiyar killace masu fama da coronavirus, shi ne mutum na farko da ya kamu da cutar a jihar Kano.
A wannan tattaunawar da ya yi da Aminiya ya yi bayani a kan zamansa a cibiyar da labarin da aka yi ta bazawa cewa da gangan ya kai cutar Kano ya yada ta, da ma wasu batutuwan na daban.
Mun ji bayanai iri-iri game da kai kan cutar corona, kuma kai ba a ji daga gareka ba. Shin ko za ka iya mana gamsasshen bayani tun daga farko har karshe?
Ni ma daga nawa bangaren akwai bayanai masu daga hankali, sai dai kamar yadda ka nema, bari na warware zare da abawarsa.
Labarin yadda na sha fama da cutar da kuma wanda ke yawo cewa da gangan na yi ta shiga jama’a alhali ina sane cewa ina da cutar corona a jikina – dukkan wadannan kanzon kurege ne da aka yada.
Har wayau kuma, batun da ke cewa wai na ziyarci Amurka kawanaki kafin na dawo Abuja inda aka yi mini gwajin da ya tabbatar da ina da cutar.
Daga nan na dangana zuwa gida Kano – wannan ba gaskiya bane.
Ziyarar karshe da na kai Amurka tun watan Satumban bara ne, a lokacin ma ba a san da cutar a duniya baki daya ba.
Ban je Kaduna ba sabanin yadda ake fada, domin bulaguron da na yi na karshe shi ne Abuja da Legas da kuma Kano – kuma duka a jirgi na yi yawace-yawacen nan.
Sai bayan kwanana 12 a Kano sai na fara jin zazzabi, wanda na sha magani; amma da ya ki ya warke, hadi da bayanan da nake ji game da coronavirus – kawai sai na kira tawagar masu kai dauki kan cutar domin su zo su mini gwaji.
A kashin gaskiya, don Allah da Annabi, ban ma cancanci a jinjina mini ba dangane da ta-mazan da na yi wajen a mini gwaji?
Kuma arashi a nan, yunkurin da na yi ya taimaka wajen ankarar da gwamnati ta dauki kwararan matakai kan yaki da cutar.
To sai bayan kwana hudu da sakamakon gwajin ya fito ne aka sanar da ni cewa na kamu da corona; inda daga nan aka kai ni cibiyar killace jama’a.
Yaya kake ji game da rade-radin da ke yawo cewa wai kai ne ka shigo da cutar corona jihar Kano?
Labaran da ke yamadidi cikin al’umma wadanda suke shafa mini bakin fenti – soki burutsu ne kawai.
Duk da cewa ni ba masanin kiwon lafiya ba ne, amma na yi amanna cewa akwai alamun cutar corona a jihar Kano tun gabanin ma a mini gwajin da ya nuna ina da ita.
Shekarata 75 a duniya kuma na yi imani a wadannan shekaru nawa, babu dalilin da zai sa in cutar da mutanen da nake kauna – mutanen jihar Kano.
Ko ina da wata hujjar cutar da wani mahaluki?
Dadin dadawa, wani ya yi tunanin wai na shigo da corona Kano, ina ga bai mini adalci ba, kuma kamar yadda na ce na shafe kwana 12 a Kano… kuma ko akwai shaidar cewa ba a Kano na kamu da cutar ba?
Ina jin takaicin karanta shaci-fadin da ake yi a kaina. An shafa mini bakin fenti, amma na bar wa Allah lamarin, tabbas Zai wanke ni daga zargin.
Da nake magana da kai a halin yanzu, an sallame ni bayan an tabbatar da ba na dauke da cutar a yanzu; kuma babu ko mutum guda daga cikin wadanda na yi mu’amala da su da ya kamu da ita bayan an sallame ni.
Ko ka damu da yadda aka yayata batun kamuwar ka da cutar ga jama’a?
Eh, na damu gaskiya. Ko da yake ba hakan yana nufin ina ja-in-ja da kowa game da batun ba ne, sai dai kawai ina jin cewa nawa batun an masa fahimta ta daban idan aka kwatanta da wasu makamantan wannan da suka faru a sassan kasar nan da kuma duniya.
Ba zan iya cewa ga dalilin da ya sa batun nawa ya zama na daban ba, inda aka bayyana wa duniya sunana da cikakken adireshina alhali kuwa ba a taba bayyana suna da adireshin wanda ya fara kamuwa da cutar a Najeriya ba.
Kawai abin da aka yi ta gaya mana, wani dan kasar Italiya ne.
Abin lura a nan shi ne, wani jami’in gwamnati ne ya bayar da bayanan nawa ga duniya kuma hakan ne silar tayar da jijiyar wuya da kuma nuna mini tsangwama – a kan laifin da ban aikata ba.
Abin ban haushi a nan shi ne, wai me ya sa aka yi wa nawa lamarin irin wannan hukuncin na daban?
Ko za ka fada mana yadda ka samu kanka a cibiyar killace masu dauke da cutar?
A tsawon zaman da na yi a cibiyar na kwana 29, ban kwanta rashin lafiya ko da na kwana guda ba, za ka tabbatar da hakan daga likitoci.
Sai dai fargabata a nan ita ce, an taba mini aiki a zuciya, wannan ne dalilin da ya sa na ce maka na je Amurka a watan Satumban bara.
Na kasance cikin fargabar yiyuwar tashin ciwon a lokacin da nake a kwance a cibiyar.
Zama a wajen gaskiya akwai dimautarwa ciki, ba wai saboda rashin likitoci ko abinci ba; amma saboda cin zarafina da aka yi ta yi da kuma kallon da jama’a suke mini.
Ina ta karanta muhawarar da jama’a ke yi a kai, musamman ma a soshiyal midiya hada da tsananin damuwa na tunanin ko mutum ya rayu ko akasin haka.
Kari kan haka, na kasance cikin kadaici a cibiyar na tsawon kwana hudu kafin a kawo mutum na biyu.
Gaskiya lamarin akwai matukar dimuwa, amma dai dukkan godiya ta tabbata ga Allah Madaukakin Sarki da Ya raya ni.
A tsawon rayuwata ba a taba zargi na da nuna tsagwaron rashin tausayi ga ’yan uwana ba.
Shin gwamnatin jihar Kano ta taimaka wajen samun warakar da ka yi?
An kula da ni matuka kuma su masu tafiyar da cibiyar sun taimaka gaya wajen kyautata zamana a can.
Sun yi kokarin samar da dukkan abin da nake bukata a saka mini a abinci – har ta kai ga a kullum sai an kira ni an tambaye ni wane abinci nake so a kawo mini, ko da yake ina yawan shan shayi a zaman da na yi a can.
An ba ni magungunan kara karfin garkuwar jiki kamar su vitamin C da sinadarin zinc.
Sannan na yi amfani da maganin gargajiya ciki har da tafarnuwa.
Ko da yake, yana da muhimmanci a jinjinawa jami’an kiwon lafiyar da suke aikin kula da masu fama da cutar saboda yadda suka sanya kansu cikin hadari.
Ko za mu iya cewa ka yafe wa wadanda suka dinga yada labaran karya game da kai?
A’a, ba zan kullaci kowa kan lamarin nan ba, amma hakan ba ya nufin na yafe musu.
Sun bata mini suna a idon mutanen da nake girmamawa; kai sun baza duk wani nau’in labaran karya a kaina.
Ka duba fa, akwai wanda ma ya yi mini kazafin cewa wai na kubuta daga harbin bindigar dan sanda a yayin da nake kokarin guduwa daga cibiyar killace masu cutar a Abuja inda na gudu zuwa Kano domin neman maganin raunin harbin bindigar da ’yan sanda suka yi mini.
Kai sun ma ce ina ta ziyartar wurare da dama domin kawai in tabbabatar da mutane da dama sun kamu da cutar corona.
Wadannan duk labaran kanzon kurege ne, kuma ba zan taba yafe musu ba – saboda yadda suka shafa mini bakin fenti.