Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya rattaba hannu a kan kasafin kudin shekarar 2022 na Naira tiriliyan N17.126 da safiyar ranar Juma’a.
Sai dai Shugaban ya nuna rashin jin dadinsa kan canje-canjen da ya ce Majalisar Dokoki ta yi wa kasafin na kare-kare da rage-rage ba tare da kwararan dalilai ba.
Daga cikin abubuwan da Shugaban ya nuna damuwa a kansu har da kara kudaden shigar Gwamnatin Tarayya da Naira biliyan 400.
Shugaban Buhari ya kuma rattaba hannu kan kudirin kasafin kudin shekarar 2021, wanda ya ce yana da matukar muhimmanci wajen aiwatar da kasafin kudin shekarar 2022.
Sanya hannu kan kudurin kasafin kudin da aka yi wa take da “Kasafin Ci gaban Tattalin Arziki Mai Dorewa”, ya samu halartar shugaban Majalisar Dattawa Sanata Ahmed Lawan, Kakakin Majalisar Wakilai Femi Gbajabiamila, Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha da kuma Ministar Kudi da Tsare-Tsare, Zainab Ahmed.
An mika wa shugaban kasa kudirin dokar ne don sanya hannu, ta hannun babban mai taimaka masa kan harkokin Majalisar Dattawa, Sanata Babajide Omoworare.
Majalisar Dokoki ta mika wa Shugaban kasa sabon kasafin kudin a ranar 24 ga watan Disamba 2021.
Shugaba Buhari ya mika daftarin kasafin kudin 2022 na Naira Tiriliyan 16.391 ga zauren Majalisar Tarayya a ranar 7 ga Oktoban, 2021 don yin nazari tare da sahale masa.