✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ban ji dadin yadda gwamnati ke yunkurin kwace mini Otel ba – Nwanko Kanu

Tsohon dan kwallon Super Eagles ta Najeriya, Nwankwo Kanu ya koka  game da yadda Gwamnatin Tarayya take yunkurin kwace masa otel dinsa mai suna Hardley…

Tsohon dan kwallon Super Eagles ta Najeriya, Nwankwo Kanu ya koka  game da yadda Gwamnatin Tarayya take yunkurin kwace masa otel dinsa mai suna Hardley Apartment da ke Bitoria Island da ke birnin Legas.

Kanu wanda ya koka a lokacin da yake hira da manema labarai a karshen makon jiya ya ce, ya yi mamakin yadda Gwamnatin Tarayya a karkashin Kamfanin Kula da Kadarori (AMCON) ta fara yi wa otel din kwaskwarima, ta hanyar yin fenti da wasu gyare-gyare duk da cewa maganar tana gaban kotu.

Kanu Nwankwo dai ya kasa biyan bashin da ya karba ne daga wajen wani banki a Najeriya, wanda hakan ya sa bankin ya kai shi kara kuma kotu ta umarci a sayar da otel din ta hannun Kamfanin AMCON.   Tun a shekarar 2015 kotu ta zartar da wannan hukunci amma Kanu ya daukaka kara zuwa Babbar Kotun Tarayya da ke Ikoyi a Jihar Legas.  Tun daga wancan lokaci aka ci gaba da sauraron karar.

A bara 2018 ne aka sake sauraron karar amma kotu ta dage zuwa ranar 31 ga wannan wata da muke ciki don ci gaba da sauraron karar.

Kanu ya ce, abin mamaki kwanaki kadan kafin a sake ci gaba da shari’ar sai ya ga wadansu daga cikin ma’aikatan Kamfanin AMCON sun shiga yi wa otel dinsa kwaskwarima ta hanyar yin fenti ba tare da sani ko izininsa ba.

Ya ce bayan da harkokin otel din suka tsaya, ya shiga mawuyacin hali wajen daukar dawainiyar masu ciwon zuciya a gidauniyarsa ta Kanu Heart Foundation, inda ya ce yanzu haka akwai kimanin marasa lafiya 500 da suke bukatar taimakon gaggawa, kuma daga kudin shigar da yake samu a otel din ne yake tafiyar da harkokin cibiyar.

Ya ce tun da otel din ya tsaya ya shiga mawuyacin hali inda sai ya hada da ’yan buge-buge da neman tallafi daga wajen ’yan uwa da abokan arziki yake samun damar daukar nauyin gidauniyar tasa. Ya ce baya ga samar wa dimbin jama’a ayyukan yi a otel din, yana samar masa kudin shigar da yake tallafa wa gidauniyarsa.

Ya ce kutsen da aka yi a otel din ya sa an sace masa da yawa daga cikin lambobin yabonsa. Ya ce a gaskiya ya fara nadamar zuba hannun jari a kasar nan, bayan gwamnati ce ta bukaci su yi haka a baya.

Ya ce wannan zai iya zama darasi ga ’yan kwallon yanzu, inda da wuya ne gwamnati ta shawo kansu wajen zuba jari a kasar nan idan suka lura da abin da ya faru da ni.

“Ban ji dadin yadda gwamnatin tarayya take yi mini haka ba a matsayina na wanda ya bauta wa kasar nan a bangaren kwallon kafa.”

Yanzu dai hankali ya karkata ne a kan ci gaba da sauraron wannan kara a Babbar Kotun Gwamnatin Tarayya da ke Legas a tsakanin Kanu Nwankwo da kamfanin AMCON a ranar 31 ga wannan wata da muke ciki.