✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ban janye wa kowa ba —Dan takarar gwanan LP a Kaduna

Dan takarar ya ce ya shirya karawa a zaben gwamnan da za a yi a ranar Asabar.

Dan takarar gwamna na Jam’iyyar LP a Jihar Kaduna,  Jonathan Asake, ya ce bai janye wa kowa takararsa ba a zaben gwamnan da za a yi ranar Asabar.

Asake ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Kafanchan, hedikwatar Karamar Hukumar Jema’a ta jihar.

Ya bayyana zargin cewa ya karbi Naira miliyan 100 daga hannun Uba Sani, dan takarar gwamnan APC da Gwamna Nasir El-Rufai don hada kai wajen kayar da PDP a ranar Asabar a matsayin labari mara tushe.

“Suna rudar mutane cewa Uba Sani ne ke daukar nauyina domin a raba kuri’un Kudancin Kaduna, don Uba Sani ya yi nasara.

“Babu wani daga cikin shugabannin jam’iyyar PDP da zai iya fuskanta ta ya nemi na janye takarata, a maimakon haka sai suka koma yin amfani da ’yan takara don ganin na janye,” in ji shi.

Ya kalubalanci jam’iyyar PDP ko kuma duk wanda ke da shaidar cewa ya karbi kudin da ya bayyana wa jama’a.

Asakwa ya ce a matsayinsa na daya daga cikin manyan masu sukar gwamnatin APC a jihar, ba zai taba shiga wata yarjejeniya ta siyasa da Uba Sani ko El-Rufai ba.

“Suna so su rudi masu zabe cewa kuri’ar jam’iyyar LP ta APC ce.

“Duk wadannan labarun karya ne. Ban taba zama ba kuma ba zan taba zama da Uba Sani da Nasir El-Rufai kan kowace irin yarjejeniyar siyasa ba.

“Ina kalubalantar kowa da ya zo da wata kwakkwarar shaidar da muka taba haduwa inda na karbi kudi a wurinsu,” in ji shi.

Asake ya yi alkawarin samar da ingantaccen shugabanci kuma abin koyi ga al’ummar Jihar Kaduna idan aka zabe shi a ranar Asabar.