Dan takarar da ya sha kaye a zaben Shugaban Kasar Kenya, Raila Odinga, ya yi watsi da sakamakon zaben da ya ba abokin takararsa, William Ruto nasara.
A ranar tara ga watan Agustan 2022 ne Hukumar zaben kasar ta bayyana William Ruto wanda shi ne mataimakin Shugaban Kasar mai ci, a matsayin wanda ya lashe zaben.
- Mutumin da ya yanke gabansa yana tsaka da mafarkin yanka nama
- 2023: Dukkan kuri’un Arewa maso Yamma na Kwankwaso ne – Buba Galadima
To sai dai kwamishinonin zabe hudu daga cikin bakwai sun ki amincewa da sakamakon har yanzu, bisa dalilinsu na cewa ya saba wa adadin kuri’un da aka kada.
Mataimakiyar Shugabar Hukumar Zaben Kasar, Juliana Cherera ta shaida wa manema labarai cewa ita da wasu Kwamishinonin zaben sun ki amincewa da sakamakon ne bisa biris da tambayoyinsu da shugaban hukumar ya yi yayin bayyana sakamakon.
Ta ce, “A ganinmu adadin da shugaban Hukumar zabe, Wafula Chebukati, ya sanar ba mai inganci ba ne, kuma kotu ce kawai za ta iya daukar mataki kansa.
“Abin da muka gani jiya tsurar karya dokokin kundin tsarin mulki ne na kasarmu.
“Kuma za mu nemi hakkinmu ta mafitar da kundin tsarin mulki ya ba mu, wato kotu,” inji Odinga.
William dai ya samu nasara kan Odinga da ’yar tazara kadan, inda ya samu kaso 50.49, yayin da Odinga ya samu kaso 48.5 cikin 100.
Wani lauya mai suna Bobby Mkangi ya ce idan Kotun Koli ta yi watsi da sakamakon zaben kamar yadda Odinga ke da muradi, za a sake zaben ne cikin watanni biyu masu zuwa.
Lauyan ya ce idan kuma ba a yi hakan ba nan da sati guda, za a rantsar da William a matsayin halastaccen Shugaban Kasar.