Shugaban Kasa Bola Tinubu, ya ce bai ga dalilin da zai sa ’yan Najeriya su riƙa rayuwa cikin talauci ba la’akari da tarin arziƙin ƙasar.
Ya kuma bukaci ’yan Najeriya mazauna Amurka da su daɗa jajircewa sannan su sake tunani kan hanyoyin samun nasara.
Tinubu ya bayar da shawarar ce yayin wani taron da ya gudanar da ’yan Najeriya mazauna kasashen waje a birnin New York na Amurka, a ranar Laraba.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito cewa Hukumar Kula da ’Yan Najeriya Mazauna Ketare (NIDCOM) ce ta shirya taron a gefen taron Babban Zauren Majalisar Dinkin Duniya (UNGA) karo na 78 da yake gudana a birnin na New York.
Tinubu ya kuma ce Allah Ya albarkaci Najeriya da dimbin arziki.
Ya ce, “Maganar gaskiya ban ga dalilin da zai sa mu rika rayuwa cikin talauci ba. Raunin shugabanci ne kawai babbar matsalarmu.
“Abin ma da na fi mayar da hankali ke nan a kai lokacin yakin neman zabe na. Zabe ne da aka fafata sosai. Amma da ban fito a jajirce ba sannan aka ga da gaske nake yi, da ba a zaɓe ni ba.
“Ni ma akwai lokacin da na taɓa yin rayuwa a kasashen waje kamar ku, don haka babu abin da zai hana ku zama kamar ni, idan kuna so matukar akwai jajircewa,” in ji Tinubu.
Shugaban ya kuma jinjina wa ’yan Najeriya da suka jajirce suka zama zakarun gwajin dafi a fannonin rayuwa daban-daban, inda ya ce irin su abin alfahari ne.
(NAN)