Kocin Arsenal Mikel Arteta, ya ce tawagar ’yan wasansa ba ta gamsu da nasarar da ta samu ta shiga rukunin kungiyoyin da za su kara a Gasar Zakarun Turai ta badi ba.
Arteta ya bayyana cewa za su ci gaba da fafatawa don neman lashe kofin Firimiyar Ingila na bana.
Arteta ya ce, “irin kwarin gwiwar da suke bukata ke nan a yanzu, musamman kwanakin karshe da suka rage kafin kammala gasar.”
Arsenal ta sha kaye a hannun Manchester City da ci 4-1 a makon da ya gabata yayin da a ranar Talata wannan makon ta lallasa Chelsea a Emirates.
Chelsea dai na ta taga-taga a gasar ta Premier ta bana, inda a yanzu take mataki na 12 da maki 39 bayan fafatawa 33.
Kamfanin Dillancin Labarai na AP ya ruwaito Arteta yana cewa “abubuwa da dama za su faru” a fafatukar neman lashe kofin Gasar ta Firimiyar a bana.
Mutane da yawa dai na ganin City ta riga ta lashe kofin a bana.