Kocin kungiyar kwallon kafa ta kasa Super Eagles Stephen Keshi a ranar Litinin da ta gabata ne ya bayyana cewa bai damu da irin sukar da wasu ke yi masa na yadda yake tafiyar da al’amarin kungiyar ba musamman yadda yake kafewa a kan bin ra’ayinsa a wajen zakulo ’yan kwallon da suka fi dacewa su buga masa kwallo maimakon bin ra’ayin wasu
Keshi ya fadawa Gidan Rediyon BBC a lokacin da ake hira da shi cewa “in dai a kan aikin horar da kungiyar kwallon kafa ta kasa Super Eagles ne zai yi iya bakin kokarinsa ne a kan abin da ya tabbatar zai kawo nasara ga kungiyar ba tare da shakkar komai ba.
“Ba zai yiwuwa a ce kowane ne ke sona a matsayin kocin Najeriya ba, dole a samu masu kaunata da kuma wadanda ba sa kaunata, don haka ni ban damu da sukar da wasu ke yi a kaina ba muddin ina tafiyar da aikina a bisa nasara”.
Da aka tambaye shi a kan rade-radin da ake yi cewa Hukumar Shirya kwallon kafa ta kasa NFF take yi na yunkurin maye gurbinsa da wani sabon koci, Stephen Keshi ya ce a shirye yake da duk shirin da hukumar take shirin yi, don tun farko bai taba tunanin zai dawwama a matsayinsa na kocin Super Eagles. ba
Ya bayar da misalin yadda a shekarar 2012 a lokacin shi da tsohon koci Amodu Shu’aibhu suka haye da kungiyar Super Eagles gasar cin kofin duniya amma aka yi watsi da su aka dauko sabon koci. Ya ce haka kuma irin haka ta taba faruwa da shi a lokacin da yake kocin kasar Togo inda kasar ta maye gutbinsa da sabon koci, don haka ba sabon abu ba ne idan aka maye gurbinsa da wani koci a wannan lokaci idan Hukumar ta bukaci yin haka.
Ban damu da sukar da wasu ke yi min ba -Stephen Keshi
Kocin kungiyar kwallon kafa ta kasa Super Eagles Stephen Keshi a ranar Litinin da ta gabata ne ya bayyana cewa bai damu da irin sukar…