✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ban Auri Hadiza Gabon Ba-Ali Nuhu

Fitaccen jarumin Kannywood Ali Nuhu ya karyata rade-radin da ake yadawa  cewa ya auri Hadiza Gabon. Dan wasan kwaikwayon wanda ake kira Sarkin Kannywood ya…

Fitaccen jarumin Kannywood Ali Nuhu ya karyata rade-radin da ake yadawa  cewa ya auri Hadiza Gabon.

Dan wasan kwaikwayon wanda ake kira Sarkin Kannywood ya fadi haka ne a tattaunawar da yayi da wakilinmu.

Hoton Ali Nuhu da Hadiza Gabon ya bazu a kafofin sadarwar zamana, inda ake cewa wai sun yi aure a Kano.

Ali Nuhu, wanda shi ne manajan kamfani FKD ya ce wadansu mutane na shirya labari wanda ba gaskiya bane ba tare da sun yi tunanin abin da zai iya jawowa ba.

Sai jarumin ya ce wannan hoton da ake yadawa na wani fim ne mai suna Akushi, inda Gabon ta fito a matsayin matarsa.

“Hoton da ake yadawa, an rubuta a jikinsa ‘daga fim din Akushi’,” Inji Ali Nuhu.