Dan takarar Shugaban Kasa a karkashin Jam’iyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar a zaben da ya gabata, a shekaranjiya Laraba ya ce zai kalubalanci sakamakon zaben da aka yi a ranar Asabar a gaban kotu.
Atiku ya fadi haka ne jim kadan bayan Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta bayyana sakamakon zaben inda Shugaba Muhammadu Buhari na Jam’iyyar APC ya samu nasara.
Shugaba Buhari ya samu nasarar lashe zaben ne da kuri’a miliyan 15 da dubu 191 da 872 yayin da Atiku Abubakar ya samu kuri’a miliyan 11 da dubu 255 da 978 ya zo na biyu.
Shugaba Buhari ya lashe Jihohi 19, yayin da Atiku kuma ya lashe jihohi 17 da Babban Birnin Tarayya Abuja. ’Yan takara 72 ne suka fafata a zaben wannan kujera.
Atiku ya ce idan aka yi la’akari da yadda aka rika yin magudi a sassa daban-daban na kasar nan a yayin zaben, hakan ya sa ba zai taba amincewa da sakamakon zaben ba.
“Abin akwai daure kai a ce jihohin da ke fama da matsalar tsaro sun fi kawo yawan kuri’u fiye da jihohin da ake zaune lafiya. Sannan ta yaya za a ce a Jihar Akwa Ibom inda nake da dimbin magoya yawan kuri’un da suka kada sun yi kasa da fiye da kashi 50 idan aka kwatanta da na zaben 2015? Wadannan da wasu dalilai na daga cikin abin da ya sa na yi fatali da sakamakon zaben”, inji shi.
Baya ga Atiku Abubakar, Jam’iyyar PDP ma tuni ta yi fatali da sakamakon zaben.
Sai dai zuwa hada wannan rahoto ba a samu labarin Atiku Abubakar ko Jam’iyyarsa ta PDP sun shigar da kara a kotu don kalubalantar zaben ba.