Assalamu Alaikum. Barkanmu da sake haduwa a cikin wannan fili. Ga cigaban bayani a kan abubuwan da ma’aurata za su aikata don tafiyar da bambancin sha’awa a tsakaninsu, da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga duk masu bukatarsa, ya kuma haifar da karuwar farin ciki da jin dadi cikin rayuwar aurensu, amin.
Hanya Ta 7: Tunatarwa Ga Ma’aurata, cigaba daga inda muka tsaya: Da wahalar Lahira… Na yi aure shekara 11 da suka wuce kuma auren soyayya domin har guduwa ta taba yi da aka ce ba za a ba ta ni ba. Kuma mun ci gaba da soyayya cikin rayuwar aurenmu na tsawon lokaci musamman a fannin ibadar aure, kusan in ce ma tafi ni dagewa ta wannan fannin. Amma ba mu fi tsawon shekaru uku ba a haka sai ta canza mani, ta daina yarda da ni idan na kusance ta, ga shi kuma ta riga ta saba min, saboda haka na kan yi mata nasiha cewa ta ji tsoron Allah kar ta sa na fada ga sabon Allah amma sai ta ce wai ta ba ni izini in je in nemi matan banza, yanzu shekara takwas ke nan mun kasance a haka, na rasa yadda zan yi da rayuwata! Daga Bakori.
Anty don Allah ki yi wa mata nasiha kan kin ba mazansu hakkinsu na ibadar aure, domin Uwargidana duk lokacin da na neme ta sai ta ce mini ba ta iyawa, in na matsa mata sai ta ce in je ga mata can waje in yi, na yi mata nasiha amma a banza, ga shi ni mai tsananin son ibadar aure ne shi ya sa na yi aure don in kaucewa zina, amma kullum ina cikin damuwa! Daga Abuja.
Don Allah Nabila ki kara kira ga mata su rika hakurin biyawa mazajen su bukata domin ni tawa matar sai ta ga dama, yanzu haka sai mu kwana talatin ba ta bari na kusance ta ba! Daga Kaduna.
Kadan ke nan daga cikin sakoannin da wannan fili ya samu daga ‘yan’uwa magidanta game da yadda matansu ke muzguna masu ta hanyar danne masu hakkin su na ibadar aure. Ga mata masu irin wannan dabi’a ta yin kiyon ibadar aure ga mazansu.
Da farko ina son ku san cewa wannan tsananin rashin kyautatawa ne da rashin sanin nauyin hakkin aure, koma mene ne dalilin da ya sa ku aikata haka din, domin kun zabi jin dadin duniya sama da na ran gobe kiyama, kun gwammace ku ji kunyar lahira a kan ku ji ta duniya.
Duk zaman me mu ke yi an an duniyar in ba zaman jiran tafiya lahirar ba? To kuma ga shi an ce bin miji shi ne hanyar tsira ranar gobe kiyama, to duk wanda ke wasa da hanyarsa ta tsira ranar gobe kiyama kuwa ya yi ganganci mai yawa. Girman miji a wajen matarsa bai da iyaka, Uwar Muminai A’ishatu (RA) ta yi mana wannan kiran: “Ya ku mata! Inda kun san girman hakkin da mazan ku ke da shi a kanku, lallai da kowaccen ku ta share dattin tafin kafar mijin ta da fuskarta!” Sannan Annabi (SAW) ya tambayi wata Sahaba RA: “Ya ki ke da mijin ki?” “Ina iyakar kokarina gare shi sai dai akan abubuwan da suka fi karfina.”
“Ki kula sosai da yadda ki ka mu’amalance shi domin shi ne aljannarki kuma shi ne wutarki.” Duk macen da mijin ta ya kira ta shimfidar barcinsu ta ki zuwa, Mala’iku za su yi ta tsine mata har wayewar gari, to ko mala’ika daya Ya tsine maka Ya ka iya da ran ka? Mu yi laakari da yadda tsinuwar uwa ke yin tasiri ga rayuwar da to ya kuma tsinuwar Mala’iku su da ba su taba sabon Allah ba? Haka nan duk matar da mijin ta yayi fushi da ita Wanda ke Sama (SWT) Zai yi fushi da ita har sai mijin ta ya bar fushi da ita, kuma duk ibadun ta ba a amsar su har sai mijin ta ya daina fushi da ita.
Allah SWT da kan Sa Ya tabbatar da tsinuwarSa ga macen da in mijin ta ya kiraye ta don ibadar aure su kan tsaya su bata lokaci har sai barci ya kwashe mijin. Haka kuma Annabi SAW ya yi umarni da cewa: In miji ya kirayi matar sa (domin ibadar aure) ta zo ko da tana bisa rakumi ne, a wani wajen kuma koda tana gindin murhun girki ne. Da wahalar lahira dai, to gara ta duniya komin tsananin ta, da fatan kunnen ku ya ji muku jin da zai tsirar da jikin ku daga wuta, amin!
Zan dakata a nan sai sati na gaba In sha Allah. Da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarsa a kodayaushe, amin.