Assalamu Alaikum. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili. Ga ci gaban bayani a kan abubuwan da ma’aurata za su aikata don tafiyar da bambancin sha’awa a tsakaninsu, da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga duk masu bukatarsa, ya kuma haifar da karuwar farin ciki da jin dadi cikin rayuwar aurensu, amin.
Hanya Ta 7: Tunatarwa Ga Ma’aurata:
Zan fara gabatar da nasiha ga mazan da matansu suka fi su bukatuwa da sha’awa, sannan sai ya kasance sun kyalesu babu kulawa, sun sharesu har sai ranar da su suka bukace su alhali suna sane da halin da matansu ke ciki na tsananin bukatuwar sha’awa, su sani yin haka zalunci ne ba jarumta ba ce!
Ya ku irin wadannan magidanta, ku sani, babban jigon da aka gina aure a kai, shi ne saduwar ibadar aure don biyan bukatar sha’awar juna, don haka in mace ta zan ba ta iya gamsar da mijinta ko miji ya zan ba ya iya gamsar da matarsa, to wannan kwakwkwaran daliline na a raba auren don ta samu wani wanda zai iya gamsar da ita. Cikar mazantakar da namiji shi ne ya kasance mai gamsar da iyalansa ta ko wane irin fanni na rayuwar su amma musamman ma ta fannin ibadar aure.
Ku sani, rayin dan adam na iya daure wa dukkanin bukatuwar rayuwar duniya, amma ban da bukatuwar ibadar aure saboda da tsananin karfin ta da girmanta. Ina amfanin auren da matanku suke yi da ku in auren bai yi masu maganin tsananin bukatuwarsu ta sha’awa ba? Sai dai su rika kallon rage zafi? Dubi irin hadarin da kuke tura matayen ku a ciki? In har kuna kaunarsu me zai hana ba za ku sadaukar da ko da sau daya a sati ba don warkar masu da tsananin bukatuwarsu?
Duk wani kayan jin dadin da za ku tanadar wa matanku ya bi bayan biya masu bukatun sha’awarsu domin shi ne babban jigon da ya hada ku a matsayin mata da miji; sannan ba wani wanda zai iya yaye masu wannan damuwa dole sai ku mazajensu. In har matsalarku ta rashin son gabatar da Ibadar Aure ta girmama ta yadda ba yadda za ku ku kasance cikin yanayin gabatar da Ibadar auren, sai ku binciki halattattun hanyoyi da da za ku bi don biya wa matanku bukatun sha’awarsu ba tare da lallai sai ku kun yi ibadar auren ba, ku sani in har kuna kaunar matanku kuma kuna son zama da su to to dole ku yi sadaukarwa gare su ta wannan bangaren. Ku tuna, in ku ne kuke cikin hali irin wanda matanku suke ciki za ku so matan naku su share, su ki ba ku hakkinku na biyan bukatar aure? Da yawan mazaje ba za su iya hakurin zama da mace mai kyuyar ibadar aure musamman in su masu yawan bukatar ibadar auren ne, don haka ku so wa matanku abin da kuke so wa kanku.
Mazantaka ba a kira, siffa ko halitta take ba. Mazantaka a kwakwalwa take, don haka in kuna tunanin ku cikakkun mazaje ne ta kowane fannin to haka za ku kasance. In kuma kuna tunanin kun cika mazaje ne ta fannin biya wa matanku bukatun masarufi kadai amma ban da bukatunsu na sha’awa to hakan za ku kasance. Sannan Ibadar aure ba biyan bukatar sha’awa ne kadai ribarta ba, tana sanya rahama da tausayi tsakanin ma’aurata kamar yadda ayoyin Alkur’ani mai girma suka yi bayani. Da fatan Allah Ya ba ku ikon gyara wannan kuskure naku, amin.
Da Kunyar Dare…
Maza mu ji tsoron Allah: mu sani cewa kamar yadda bayar da abinci, muhalli, sutura, kula da lafiya, kare mutunci da koyar da addini suka wajaba a kan dukkan namijin da ya auri mace, to haka wajibcin biya mata bukatar ibadar aure ta wajaba. ‘Yan’uwana kar mu manta, sha’awar ibadar aure ita ce ginshikin ginin duk wani aure to mene ne dalilin da sashe zai saba wa sashe a kan haka? Rashin kula mace da ibadar aure har na wasu watanni ba daidai ba ne, saboda haka idan ba za ku iya ba, ku sallamesu su nemi halas a gaba, maimakon ku bar su suna neman surka halas da haram. Allah Ya kare mu, amin.
Bayan haka mazaje ku sani, kamar yadda neman dukiya domin tsira da mutunci ya zama wajibi, haka neman magani ya zama wajibi ga duk magidanci mai fama da matsala ta wannan fannin. Magidanta ku farga ku gane cewar ci ko shan duk abin da aka gani ba dabara ba ce, ba kuma jin dadi ba ne, ya kamata a san abincin maza a san na mata. Idan kuma akwai matsala a yi tambaya kar a ji kunya, mu san cewa da kunyar dare gara ta rana ga duk namijin da ya san ciwon kansa!
… Daga wani Bawan Allah.
Sai sati na gaba Insha Allah, Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a kodayaushe amin.