✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bambancin sha’awa a tsakanin ma’aurata (3)

Assalamu Alaikum, barkanmu da sake haduwa a cikin wannan fili, ga cigaban bayani a kan abubuwan da ma’aurata za su aikata don tafiyar bambancin sha’awa…

Assalamu Alaikum, barkanmu da sake haduwa a cikin wannan fili, ga cigaban bayani a kan abubuwan da ma’aurata za su aikata don tafiyar bambancin sha’awa a tsakaninsu, da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga duk masu bukatarsa, ya kuma haifar da karuwar farin ciki da jin dadi cikin rayuwar aurensu, amin.

Hanya ta 3: Muhimman Abubuwa 5 da Ma’aurata suka mance:

Akwai wasu muhimman abubuwa da yawancin ma’aurata kan mance da shi a cikin rayuwar auren su:

1. Abu na farko shi ne mancewa da wani sirri mai maganin kowace irin matsala komai girmanta ko karfin tasirinta cikin rayuwar aure, in da ana kiyayewa da wannan muhimmin sirri ma, tun farko da wuya matsala mai girma ta baibaye rayuwar auren ku: wannan sirri kuwa shi ne na sa Allah Madaukakin Sarki sama da komai cikin rayuwar aure, da dagewa wajen yin abubuwan burge Allah da neman kusancin Sa sama da sauran harkokinmu na rayuwar yau da kullum. ma’aurata su kasance cikin soyayyarsu da kaunarsu da zamantakewarsu, sun sanya Allah da abubuwan neman kusancin Allah, da haka da wuya su shiga cikin matsala ko halin kaka- ni- ka-yi cikin rayuwar aurensu. Misali su rika gasar haddar wata Surah cikin Alkur’ani Mai Tsarki, ko su rika yin azumin tadawwa’i tare, ko yin tsayuwar dare tare, da taimakon juna wajen aikata ayyukan alheri da guje wa sabon Allah.

Haka kuma duk lokacin da wata matsala ta kunno kai, maimakon a yi ta bin malamai da shan magungunan da ba a san kansu ba, a koma ga Allah Madaukakin Sarki, a dage da yin addu’a cikin kankan da kai da imani, cikin yardar Allah za a ga waraka daga wannan matsala.

Maimakon a yi ta rokon Allah arziki da daukaka, sai a roke Shi dorewar  farin ciki da soyayya cikin rayuwar aure; misali, ga ma’auratan da suke fama da wannan matsala ta bambanci sha’awa, duk cikin Sujadar Sallar su sai rika rokan Allah:

“Ya Allah kai ne Ubangijinmu, kuma bayin ka ne, kai ne gatan mu, ba mu da wata gata bayan kai, Ya Allah ka gyara mana abin da ya yi tasku cikin rayuwar aurenmu, Ya Allah Ka ruruta wutar sha’awa tsakanin mu ta yadda za mu samu natsuwa da kwanciyar hankali da juna…” da sauran duk abin da suka ga yakamata su fadi na daga bukatunsu.

Sannan ga macen da take fuskantar matsalar rashin motsuwar sha’awa, duk cikin sujadar kowace Sallar da ta yi sai ta roki Allah cikin kankan da kai: “Ya Allah, Ubangijina, Kai ne Rayayye Mai Rayawa, Mai Kashewa, Kai ne Mamallakin Sama da kasa kuma Ubangijin Al’arshi Mai Girma, Ya Allah Ka wadatani da wannan rahama da ake ji lokacin Ibadar aure, Ya Allah Ka gyara mani ko mene ne a jikina ko a halayyata da ke hana ni jin abin da yakamata in ji lokacin da na kadaita da maigida…” sai ta cike da duk abin da ta ga yakamata na daga bukatunta ta wannan fannin.

Sannan koyaushe za a yi addu’ar nan da ma kowace irin addu’a to a bude da salatin Annabi SAW a kuma rufe da shi sannan a rokar wa dukkan Musulmin duniya masu irin wannan matsala waraka daga matsalar su, Insha Allah za a ga canji cikin kankanin lokaci, amma sai an dage kuma an cije, ba wai a fara a daina ba ko kuma a yi yau, gobe a yi fashi, da fatan Allah Ya amsa mana duk bukatunmu na alheri, amin.

2. Abu na 2 shi ne mancewar da Ma’aurata suka yi na cewa Allah SWT bai halatta aure don a sha wuya ko a zauna cikin kunci, bakin ciki da tashin hankali ba, Allah Ya halatta aure ne don a ji dadi kuma a more a cikinsa, saboda haka ba wani dalilin da zai sa ma’aurata su yi ta zama cikin kunci da kaka- -ni-ka-yi a dalilin wata matsala da take damun rayuwar aurensu, ya zama wajibi garesu su mike tsaye haikan don ganin sun kawar da wannan matsalar komai girmanta ko kankantarta, yakamata ma’aurata su sa dorewar farin ciki cikin rayuwar aurensu sama da komai a wajen mahimmanci.

Sai sati na gaba Insha Allah. Da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a kodayaushe, amin.