Fafaroma Francis na 16 ya ce bambancin addini da Ubangiji Ya kaddara a tsakanin al’umma ba illa ba ce, hasali ma arziki ne, yana mai kara nanata bukatar nuna kauna a tsakanin al’umma na kowace kasa da kuma kowane addini suke bi.
Farfaroman ya fadi haka ne a cikin sakon da ya saba gabatarwa na Kirsimeti duk shekara ranar 25 da watan Disamba. A cikin sakon da ya karanta a Dandalin Saint Peter a gaban dimbin mabiya Darikar Katolika, ya ce bambance-bambancen da ake da su ba illa ba ce, arziki ne.
Fafaroma,wanda ke jagorantar darikar Kirista mafi girma, mai mabiya sama da biliyan 1.3, ya yi kira ga kasar Siriya ta tuna ’yan uwantakar da ke tsakanin al’ummarta bayan shafe shekaru ana yaki.
Haka Fafaroma ya yi fatan tsagaita wutar da aka cimma a Yemen za ta kawo sauki ga wadanda yaki da yunwa suka jefa cikin kunci.
Sai kuma ya yi fatan za a rika farfado da tattauna batun zaman lafiya a tsakanin Isra’ila da Falasdinu domin kawo karshen yaki a tsakaninsu.
Haka nan ya yi tsokaci kan miliyoyin ’yan gudun hijirar Afirka da ke bukatar taimako, tare da fatan kyautatuwar dangantakar da aka samu a yankin Koriya za ta kara karfi.