Assalamu Alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili. A yau kuma, insha’Allah, za mu fara amsa tambayoyin da masu karatu suka aiko da suka danganci kayyade iyali da tazarar haihuwa. Da fatan Allah Ya sa amsoshin nan su isa ga masu bukatarsu, musamman wadanda suka aiko da su, amin.
Assalamu Alaikum, Duniyar Ma’aurata don Allah ku yi mana bayani game da bambancin ma’ana tsakanin kayyade iyali da tazarar haihuwa da hukuncin kowannensu a addinance, tare da bayanin hanyoyin da ake bi wajen aiwatar da kowanne daga cikinsu.
Amsa: Lallai kam akwai bambancin mai fadin gaske tsakanin kayyade iyali da tazarar haihuwa, musamman ta fuskar hukuncin kowannensu a addinance.
kayyade iyali shi ne wata hanya da ma’aurata za su bi wajen dakatar haihuwa ta dindindin a rayuwarsu. Wasu ma’auratan na yin haka bayan samun iyakar ’ya’yan da suke bukata, biyu, uku ko hudu, wasu kuwa na iya yi don ma kada su samu haihuwar gaba daya.
Hukuncin kayyade Iyali:
A bisa dimbin hujjoji daga Alkur’ani da Sunnar Manzon Allah SAW, da kuma sharhi da bayanan manyan malaman Musulunci, bai halatta ga ma’aurata Musulmi su kayyade yawan ’ya’yan da suke son haihuwa a tsawon rayuwarsu, ba tare da wani kwakkwaran dalili ba, kamar in dawainiyar daukar ciki ko haihuwa na sanya rayuwar matar cikin hadari, to a nan ma’aurata na iya dakatar da haihuwarsu don ceton rayuwar ita matar. Amma in ba a kan wannan dalili ba, ba wani dalilin da ke halarta kayyade iyali a addinance.
Don haka ba a kayyade iyali a dalilin tsoron talaucin iyayen da zasu haifa, ko talaucin abinda za a haifa: Allah Yayi hani ga aikata haka a wurare biyu cikin Al’kur’ani mai girma a cikin Suratul An’am, Aya ta 151:
“Kuma kadda ku kashe diyanku domin talauci, mune muke azurta ku, ku da su.” Wannan Aya mai albarka tana magana ga masu tsoron talaucin da haifuwar ‘ya’ya da yawa ka iya jawo masu.
Da kuma Suratul Isra’i, Aya ta 31:
“Kuma kada ku kashe ’ya’yanku domin tsoron talauci; Mu ne ke azurta ku da su. Lallai ne kasha su ya zama kuskure babba.” Wannan kuma tana magana ga masu tsoron talauci ga ’ya’yan da za su haifa.
Haka kuma Annabi SAW ba umarnin a yi aure kadai ya yi ba, amma Ya kasance yana cewa: “Ku auri matan da suka iya soyayya kuma masu haihuwa, don in kasance wanda ya fi sauran Annabawa yawan al’umma ranar Lahira.”
Sannan aure da tara iyali dabi’a ce ta Annabawan Allah gaba dayansu, kamar yadda Allah SWT Ya fada mana a cikin Aya ta 38 cikin Suratul Ra’ad:
“Kuma Lallai ne hakika Mun aika wadansu Manzanni daga gabaninka, kuma Muka sanya matan aure a gare su da zuri’a…”
Wadannan manyan bayin Allah, su ne suka fi dacewa ga zama abin koyi ga dukkan Musulmi, ba soye-soyen zukatan Turawan Yamma ba da ba su da tabbas.
Haka kuma a Musulunci, tara zuri’a yana daya daga cikin abubuwan morewa da jin dadin rayuwar duniya, kamar yadda Allah SWT Ya bayyana mana a cikin Alkur’ani mai girma, Aya ta 46 cikin Suratul Kahf:
“Dukiya da ’ya’ya su ne kawar rayuwar duniya…”
Haka ma a cikin aya ta 73, Suratul Nahl:
“Kuma Allah Ya sanya muku matan aure daga kawunanku, kuma ya sanya muku daga matan aurenku ’ya’ya da jikoki, kuma Ya azurta ku daga abubuwa masu dadi. Shin fa, da karya suke yin imani, kuma da ni’imar Allah, su, suke kafirta.”
Don haka, kin yin aure don gudun duniya, da kin yin aure da nufin ibada, da kuma dandake maraina don kashe sha’awa ga maza, duk haramun ne, bai halatta ga Musulmi su aikata su ba. Haka kuma bai halatta Musulmi ya kudurta cewa shi daga ’ya’ya kaza ba zai kara ba sun isa haka nan.
Hanyoyin da ake bi wajen kayyade iyali na dindindin, guda hudu ne:
1. basectomy: Wannan wani karamin aikin fida ne da ake yi ga namijin da yake son dakatar da haihuwar shi har abada; ana datse hanyar da ruwan maniyyi ke bi ya fita daga ’ya’yan maraina zuwa al’aura.
2. Hysterectomy: Shi ne aikin fida da likitoci ke yi don cire gaba daya mahaifar macen da ta bukaci dakatar da haihuwarta har abada.
3. Tubal Litigation: Shi ma aikin fida ne da ake yi don datse hanyar da kwayayen haihuwar ’ya mace ke bi su isa mahaifa, don haka in an yi, maniyyin namiji ba zai iya isa gare su ballantana har a samu shigar ciki.
4. Essure: Shi ma wani sabon tsarin kayyade iyali ne, wanda ake gabatar da shi ba tare da lallai sai an yanka mai bukatar ba, za a shigar da wani sinadari har ya isa zuwa ga hanyoyin kwayayen ’ya mace (fallopian tube), wannan zai haifar da tsiron da zai yi girma har sai ya toshe hanyoyin ta yadda kwayayen ba za su iya fita ba ballantana su isa ga mahaifa.
Don haka ’yan uwa sai mu kiyaye, duka wadannan hanyoyin dakatar da haihuwa na dindindin bai halatta ga musulmi ba, sai dai in akwai kwakkwaran dalili da ya jaza yin haka, kamar don neman lafiya, ko don ceton rai. Da fatan Allah Ya ba mu ikon kiyayewa, amin.
Sai sati na gaba sauran bayani na zuwa game da tazarar haihuwa. Da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarsa a kodayaushe, amin.